Min menu

Pages

Wannan App din na masu karatun Alqura'ani ne...

Wannan App din na masu karatun Alqura'ani ne...



 Masu karatun Alqura'ani ya kamata ku dauko wannan App din domin zai taimaka muku sosai..


Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu a yau cikin shirin namu munzo muku ne da wani bayani akan wani application mai matukar kyau wanda nasan zai birgeku sosai.


Shidai wannan application din na karatun alqura'ani ne sannan zai taimaka sosai ga masu koyo domin yanada bangare guda hudu a cikinsa.

Na farko daga cikin bangaren yana koyar da duk wasu harrufa ne daga alif zuwa karshe da yadda mutum zai iya furtasu.


Na biyu kuma yana koyar da wasali ne da kuma iya jera haruffa su hadu su bada jimla da kuma dauri da sauransu.


Sai bangare na uku inda ake koyar da yadda mutum zai furta haruffa daidai da kuma ka'idar furta karatun Alqura'anin..


Bangare na hudu kuma yadda ake karatun alqura'ani ne dalla dalla...


Haƙiƙa duk wanda ya mallaki wannan application din zai karu sosai da sosai domin zai koyi abubuwa masu yawa ko kuma ya gyara abubuwan daya manta.


Ku duba kasa za kuga gurin download din app din.


                     Download app 

Comments