Min menu

Pages

Wasu guraren bauta da akafi yawan ziyara a Duniya

 Wasu guraren bauta da akafi yawan ziyara a Duniya



Kasancewar Duniya tanada fadi tare da yawan mutane wannan yasa aka samu addinai kala kala to saidai ko cikin addinan guda uku sune kan gaba a Duniya a halin da ake ciki yanzu kuma sune ke dauke da mafi yawan mutane..


Kamar yadda addinan suka rabu hakama guraren bautarsu yake a rarrabe, ina nufin kowa akwai gurin da suka ware domin yin ibadarsu.

Dan haka zamu kawo muku jerin wasu kasaitatun guraren bauta wanda bincike ya nuna anfi yawan ziyarsu duk shekara dan haka muje cikin shirin.


Ka'aba:- Dakin ka'aba shine ya zamto na farko a jerin guraren da akafi yawan ziyarta domin gabatar da ibada a duk shekara.

Guri ne da musulman duniya ke zuwa domin sauke farali, an nuna gurin a matsayin guri mafi soyuwa a zukatan kowanne musulmi, sannan guri ne da yake tara miliyoyin mutane.


Gurin yana garin Makkah ne a Saudi Arabia.

2 River Ganges:- Shima wannan wani guri ne da masu addinin Hindu ke kaiwa ziyara domin yin bauta, kamar yadda musulmi ke ziyartar saudia dakin ka'aba haka suma masu addinin Hindu ke ziyartar wannan gurin.

Sunyi imani da cewa duk wani daya taba wannan gurin to za'a kankare masa zunubansa, sannan mutane masu yawa suna ziyartar wannan gurin.


Jerusalem:- Guri na uku shine Jerusalem shima wannan gurin yana daga cikin guraren da ake ziyarta domin bauta, masallacin qudus kenan, anan masu addinin nasara ke zuwa domin gabatar da ibadarsu, sannan guri ne da kusan ake ta samun sabani tsakanin musulmai da kuma masu addinin nasara kowa na nuna cewar nasa ne.


Gurin yana birnin qudus.


Mu kasance tare daku a wani sabon shirin.


Comments