Min menu

Pages

Abubuwan birgewa game da kasar Nigeria

Abubuwan birgewa game da kasar Nigeria.Akwai abubuwa na birgewa masu tarin yawa wanda kasar Nijeriya take dasu wanda kusan ba kowacce kasa bace take da irin wadannan abubuwan ba a nahiyar Africa dama sauran kasashen duniya baki daya.


Nigeria kasa ce da take da manyan abubuwa na gani na fada, wannan yasa a Africa take zuwa ta farko a wasu abubuwa idan har za'a kwatanta ta da sauran kasashen.


Yau cikin shirin namu muna tafe ne da jerin abubuwa kala kala wanda kasar Nijeriya take dasu na birgewa.


✓ Yawan jama'a:- Ko kunsan kasar Nijeriya tana ta daya daga cikin kasashe mafiya jama'a a kaf Africa? Wannan ma wani abin birgewa ne domin kasar tayiwa sauran kasashen fintinkau ta bangaren mutane.


✓ Yaruka masu yawa:- kasar Nijeriya tanada yare da yan kasar suke amfani dashi yakai dari biyar, wannan shine ya bada tabbacin tanada kabilu masu yawa wanda da wuya a samu kasar da ta kaita ko kuma ta fita a yawan kabilu.


✓ Masu arziki da tarin dukiya:- Akwai mutane masu matukar arziki a kasar wanda kusan babu kasar da ta tara masu arziki kamar Nigeria a yanzu domin mutum na farko da yafi kowa arziki a Africa dan kasar ne wato Aliko dangote.


✓ Wayewa:- Kusan da wuya cikin kasashen Africa a samu kasashe goma ko biyar da yan kasar suka fi yan Nijeriya wayewa domin duk wani guri a duniya da wuya kaga ba'a damawa da dan Nigeria a ciki.


✓ Malaman addini:- Idan batun tarin malamai ake to Nigeria tana sahun farko a duniya baki daya bama Africa ba, domin akwai malaman addini masu yawa a kasar.


✓ Kasuwanci:- Kusan Nigeria ce cibiyar kasuwanci a Africa duk da akwai kasashen da suma ba a barsu a baya ba amma dai Nigeria tanada hanyoyin kasuwanci masu yawa domin tana fitar da albarkatun kasa zuwa kasashen ketare.


✓ Jami'an tsaro:- Kusan Nigeria tanada jami'an tsaro na bangarori da dama wanda kusan kaf Africa babu kamarta.


✓ Masu amfani da wayar hannu:- An fibayyana kasar Nijeriya a matsayin kasar da mutanen cikinta masu yawa ne ke amfani m da wayar hannu wannan yasa aka samu matasa masu dinbin yawa suke ci kuma su sha ta bangaren yin kasuwanci da wayoyin hannunsu.


√ Kyawawan mata: Nigeria na daya daga cikin kasashe da suka tara mata masu kyau fasali da diri sannan da tsafta, duk da a Africa akwai kasashen da suka fita mata masu kyau amma dai idan za'a lissafa kasashe masu mata masu kyau to akwai Nigeria.


Wannan sune kadan daga cikin abubuwan birgewa a kasar Nijeriya dan haka ku bayyana mana sauran ta akwatin comments dinku.

Comments