Min menu

Pages

Hanyar da zaka turawa mutum sako ta WhatsApp ba tare da kayi saving din number sa ba.

 Hanyar da zaka turawa mutum sako ta WhatsApp ba tare da kayi saving din number sa ba.Abin yana ciwa mutane da yawa tuwo a kwarya wajen ganin idan zasu turawa mutum sako ta WhatsApp wai dole sai sunyi save din number wayarsa tukun zasu samu damar tura masa sako, domin babu wata hanya da mutum ke bi kai tsaye ya turawa wani sako ta WhatsApp idan bashi da wannan number a contact list dinsa dole sai yayi saving din number tukunna.


Wani ma daga ya tura sakon sau daya shikenan bazai sake yiwa mai wannan number magana ba domin dama wannan sakon da zai tura masa shine har yasa yayi saving din number, wasu suna iya goge number koda sunyi saved din number amma wasu basa iya samun damar gogewa, wannan yasa wasu sai kawai suna ganin sunayen mutane akan contact list dinsu amma su gagara gane masu number, wasu sai suna kira suna tambayar waye suna cewa sunga number ne akan wayarsu amma sun kasa gane waye.


Haka zalika yanzu muna cikin wani lokaci wanda mutum yana cikin tafiyarsa ma sai wani ya tare shi sannan ya bashi number wani tare da photo ko wani yace dan Allah ya taimaka ya turawa mai wannan number ta WhatsApp, dole sai kayi saving din wannan number tukunna zaka samu damar tura masa.


To yau ga wata hanya mai sauki da zaku bi wajen turawa mutum sako ta WhatsApp ba tare da kunyi save din number ba.

Wasu yan hanyoyi ne kadan wanda basu da yawa gasu kamar haka.

√ Kai tsaye mutum zai bude telegram dinsa sannan saiya rubuta OPEN IN WHATSAPP zasu rubuta masa a sama sai mutum ya zabi na farkon da suka rubuta zamu ajiye muku screen shot din tare da alamar a kasa.√ Bayan mutum ya shiga zasu rubuta masa START a ciki kai tsaye saiya danna gurin daga ya danna start din.


Zasu tura masa sakon cewa yanzu zai iya tura sako ta WhatsApp amma saiya danna wani guri a kasa da aka rubuta start sannan sai wani guri da zaka sa numberWanda yake so ya turawa sakon a kasa, to abinda ake so sai kasa number a kasa amma ka tabbatar kasa da code din kasa kamar haka+234 idan number Nigeria ce zaka turawa sakon sannan saika danna open chat√ Daga kasa zasu nuna maka ta WhatsApp kake son tura sakon ko ta chrome, kai tsaye saika zabi WhatsApp shikenan zasu nuna maka cewar ga gurin da zaka tura sakon shikenan saika duba sauran bayanan a kasa.


Sai ya zabi wannan


Shikenan sai nan


Daga nan saika tura sakon ba tare da ka ajiye number ba


Comments