Min menu

Pages

Kada mace tana shafawa gabanta wadannan abubuwan sunada hatsari sosai

 Kada mace tana shafawa gabanta wadannan abubuwan sunada hatsari sosaiKina mace karki kuskura kina sanya wannan abubuwan a gabanki domin suna da matsala


Barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya aiki ya hakurin kasancewa tare damu, hakika muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu a koda yaushe muna godiya sosai da sosai.

A yau cikin shirin namu zamu kawo muku wasu abubuwa ne da bai kamata mace tana sanyawa a gabanta ba saboda suna da hatsari sannan suna kawo ciwo ko kuma cuta ga mace musamman idan ta juri sanyawa a gabanta dan haka ba bata muku lokaci za muyi ba, muje cikin shirin.


Man shafawa Vaseline, bincike ya nuna Vaseline yana kawo illa ga mata idan suna sanyashi a cikin gabansu domin mafiya yawa daga cikin mayukan shafawa suna dauke da sinadarai wanda kan iya bawa mata matsala idan suna sanyawa, dan haka a shawarce duk wacce take da dabi'ar sanya Vaseline a gabanta ta daina idan har ba wanda aka iyo shi takanas dan gurin ba, domin akwai magunguna masu kama da Vaseline da ake amfani dasu to wannan babu damuwa, amma inka dauke wadannan to mace ta kiyayi amfani da sauran mayukan.


Turare:- Mata suna daukar wata sara na sanyawa gabansu ko fesawa gabansu turare domin gudun wari wanda kuma hakan ba karamin kuskure bane suke aikatawa wanda yakan iya shafar lafiyar jikinki domin sanya turare a gaba kan jawo kwayoyin cututtuka wanda zasu wahalar da mace, dan haka a shawarce ku daina sanyawa domin akwai magunguna da yawa da aka iyo domin su hana gaban mace wari kuma suna tsaftaceshi dan haka sune ya kamata ku nema kuyi amfani dashi.


Mun gode da kasancewa tare damu.

Comments