Min menu

Pages

Wani dan ball da aka kashe saboda yayi own goal

 Wani dan ball da aka kashe saboda yayi own goalKo kunsan dan wasan da aka kashe saboda kawai cikin kuskure yaci garinsu.

Ga labarin wani dan kwallo Mai suna Andres Escobar daya sadaukar da komai nasa domin kyautatawa kasar sa ta bangaren kwallon kafa da kuma kuma kudinsa.

Dan kwallo ne da ake ji dashi a lokacin a kasar ta Columbia wanda yayi suna saboda iya taka ledarsa.

To wata rana wani wasa ya hadasu da wata kasar kuma wasan mai zafi ne, an garo wata ball yaje zai ture ta cikin rashin sa'a sai kwallon ta shiga ragarsu wanda wannan shine sanadin rashin nasararsu.

Wannan abin ya bawa mafiya yawa daga cikin yan kallon haushi.

Duk wani bada hakuri babu wanda dan wasan mai suna Andres  Escobar baiyi ba domin mutane su fahimce shi, amma daga karshe suka kasa fahimtarsa.

Bayan tashin wasan da wasu kwanaki Andres Escobar yana zaune akan motarsa a wani guri saiga wasu mutane su uku sun nufo inda yake suka bude masa wuta.

Ku kalli bidiyon a kasa
Comments