Min menu

Pages

Naziru sarkin waka ya fitar da bidiyo a fusace akan zaluncin da ake yiwa tsofi a kannywood

Naziru sarkin waka ya fitar da bidiyo a fusace akan zaluncin da ake yiwa tsofi a kannywoodBidiyon Naziru sarkin waka yana yiwa yan kannywood wankin babban bargo akan kalaman ladin cima
Naziru sarkin waka ya fitar da bidiyo a fusace akan zaluncin da ake yiwa tsofi a kannywood

Naziru sarkin waka ya sake kunno wuta game da Cece kucen da ake akan tsohuwar da tace ana bata dubu biyu..


Dazu gidan jaridar BBC ta tattauna da wata tsohuwa mai suna LADIN CIMA inda har ta kada baki tace ba'a taba bata kudin da yakai dubu ashirin ba duk lokacinda aka je yin shooting da ita.

Wannan maganar da tsohuwar ta fada ta jawo maganganu masu waya gurin mutane har wasu suka fara zagin daraktoci da producers dake cikin masana'antar kannywood akan rashin kyautawar da suke.

To saidai wasu daga cikin directors din sun fito sun karyata cewar basu taba bewa wannan tsohuwar kudin da yayi kasa da dubu ashirin ba duk lokacinda suka sanyata a cikin film dinsu.

To saidai ana cikin wannan maganganun ne saiga bidiyon naziru sarkin waka ya fito yana gaskata maganar wannan tsohuwar yana cewa maganar data fada gaskiya ne harya rantse da girman Allah akan cewa idan ba gaskiya bane suma sauran su rantse.

Daga karshe ya soki duk wasu producers da directors akan rashin kyautawar da suke, sannan yace suna sane da duk abubuwan da ake a kannywood din na rashin kyautatawar.

Sannan ya kara da cewar bai kamata dan tsohuwa ta fadi gaskiya suyi mata caa a kanta ba, dame za taji da rashin kyautatawar da akai mata zata ji ko kuma da maganganun su.

Yace yana sane da yadda ake abubuwa marasa kyau a kannywood din domin wasu ma ba'a basu komai haka wasu ma sune suke biyan kudi dan kawai za'a sanya su a film.

Ga abinda yace
👇

Comments