Min menu

Pages

Ladin Cima Haruna: "Naira Duba Biyu Ake Bani Idan Nafito A Film Din Kannywood"

Ladin Cima Haruna

Ladin Cima Haruna: "Naira Duba Biyu Ake Bani Idan Nafito A Film Din Kannywood"

Wata kura ta tashi bayan BBC Hausa sunyi hira da wata tsohowar jarumar masana'antar shirya fina finan Hausa (Kannywood) mai suna Ladin Cima Haruna, a cikin tambayoyin da bbc tayiwa jarumar wanda tashafe tsawon shekaru 50 tana harkar film din hausa tafadi wani abu wanda ya hargitsa kafafen sada zumunta

Ladin Cima Haruna tace tunda take fitowa a fina finan Kannywood ba'a taba bata Naira dubu hamsin ba, tace kudin da ake bata idan tafito a film shine dubu ashirin, dubu goma ko dubu biyar, "Yanzu yau din nan naje shooting wallahi dubu biyu aka bani" Inji Ladin Cima

Sai dai wannan magana ta tada kura sosai, domin kuwa jaruman Kannywood da kuma masu shiya fina finai a kungiyar sun fito sunyi mata martani,

Martanin Ali Nuhu Ga Ladin Cima Haruna

Jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewa aikinsa na karshe da yayi da Ladin Cima cikin sabon film dinsa dayake nunawa yanzu haka mai suna Alaqa Naira dubu 40k yabiyata, kuma kamar yadda yace a cikin kwana uku kacal tasamu wannan kudin

Martanin Falalu Dorayi Ga Ladin Cima Haruna

Shima director kuma jarumi Falalu Dorayi ya musanta maganar wannan tsohuwa, yace aduk aikin dayayi da ita bai taba biyanta kudi kasa da Naira 20k ba, wasu jarumai dadama suma sunfito sunyi mata martani kuma sunce wannan magana data fada ba gaskiya bane

Naziru Sarkin Waka Ya Goyi Bayan Ladin Cima Haruna

Sai dai shahararren mawaki kuma mai shirya fina finan Hausa wani lokaci Naziru Sarkin Waka yace abin da matar tafada gaskiya ne, haka yawancin masu shirya fina finan Kannywood suke biyan tsoffin jarumai Naira 2k zuwa 5K

Yace bai kamata a nuna cewa abin da Ladi tafada karyane ba bayan kuma abin haka yake faruwa sai dai kin Allah yahana fadin gaskiya, kamata yayi a gyara irin wadannan matsaloli domin dukkan jarumai suna samun abin daza suyi alfahri dashi sanadin fitowar su a fina finan Hausa

Comments