Min menu

Pages

ME KUKA SANI GAME DA HOTON MATAR DA TA KE JIKIN NAIRA ASHIRIN?

 ME KUKA SANI GAME DA HOTON MATAR DA TA KE JIKIN NAIRA ASHIRIN?




Ita dai wannan mata ta kasance fasihiyace gurin ƙere-ƙeren tukwanen kasa da musu zane da kwalliya mai ɗaukar hankali.


Sunan ta ladi kwali an haifeta ne a garin kwali a shekara Alif dubu ɗaya da ɗari tara da ashirin, in da yanzu ake kiran garin da Abuja.



Ita dai ladi kwali ta kasance ta taso tun tana karama da san kere kere da ya danganci ƙasa haka ya sa bayan ta mallaki hankalin kanta sai hakan ya zama mata tamkar sana'a in da daga ko ina daga garin kwali har ma da makotansu ya kasance kayan ta ake rububi in da duk lokacin da ta ƙera wani  sabon abu zaka ga mutane na rububin abun kama daga tukwane, tulun ruwa, kofuna, akushi na cin abinci. 

Duk wani kayan aiki da ake anfani da shi a gidan sarautar Kwali wato Abuja a yanzu da kayan da ladi ta kera ake amfani.


A shekara 1950 Michiel Cardewan ya ga sunfurin kayan ladi kwali a lokacin da ya kaima sarkin Abuja ziyara, in da ya yaba kwarai da basirarta da baiwarta hakan ya sa ya nemi da ya ganta in da daga nan ya sata a wani makarantar fasaha da kere kere da ya buɗe a garin abuja, bayan nan kuma ta yi aiki da kamfanin kere kere dake ƙasar Amurka in da cikin lokaci ƙankani tayi fice a duniya ta hanyar kayan ƙere ƙeren ta, bayan gabatar da ita da akayi  1960 lokacin samun ƴancin ƙasarta.


Sannan ta nuna wasu daga cikin kayan da ta ƙera a wata ziyara da ta kai birnin London, in da aka bata ƙyautar karamawa ta farko ga wacce tayi fice a fanni ƙeree kere.


Duk kasancewar ta wacce ba tai makaranta ba Amma jami'ar Ahmadu Bello univeraity sun karramata da takardar degree a fanni ƙere ƙere a shekarar 1977.


In da aka ƙara ƙarramata da shedar karramawa ta NNOM a shekarar 1980.

Comments