Min menu

Pages

Magunguna biyar kada mace ta kuskura tasha idan har tanada ciki.

 Magunguna biyar kada mace ta kuskura tasha idan har tanada ciki.



Akwai jerin magunguna da mata masu ciki aka amince su sha domin karin lafiyarsu da kuma jaririn dake cikin cikinsu, sannan akwai wasu kayayyaki na marmari da ake bukatar duk wata mai ciki tana amfani dasu domin samun cikakkiyar lafiya ga jikinsu tare da jaririnsu.


To yau cikin shirinmu zamu kawo muku jerin wasu magunguna wanda ba'a so mace tayi amfani dasu idan har tanada juna biyu Dan haka kai tsaye ga jerin magungunan.


1 Warifin Wannan wani magani ne da ake amfani dashi a bangaren blood clotting, ko kadan ba'a son mace tasha wannan maganin idan har tanada ciki.


2 Clonazepam Shima wannan maganin magani ne ga mutanen da suke da cuta ta yawan damuwa da kuma abinda ya shafi kwakwalwa, shima an hana mace mai ciki yin amfani dashi domin zai iya bata cikin.


3 Ibuprofen Wani magani ne da yake kashe ciwo ko kuma wanda mutane suke sha idan sun gaji ko kuma wani guri yana musu ciwo, an hana mata masu ciki shan wannan maganin domin yana saurin zubar musu da ciki idan sun sha.


4 Ciprofloxacin Shima wannan antibiotic ne an hana mace mai ciki shan wannan maganin saboda zai takura kashi da kuma tsokar jaririn dake cikin mahaifa sannan kuma zaisa uwa taji ciwo kuma zai iya yin damages na wasu nerves din ta.


5 Primaquine Shima wani magani ne da ake amfani dashi wajen maganin malaria wacce cizon sauro yake kawo wa. An hana mai ciki amfani da maganin ne domin bincike ya nuna yana lalata fetus.




Comments