Min menu

Pages

Idan mace ta hadu da Namiji Mai Irin Wadannan Halayen to ta rikeshi gam ta samu Mijin Aure

Idan mace ta hadu da Namiji Mai Irin Wadannan Halayen to ta rikeshi gam ta samu Mijin AureKaman yadda muka kawo wasu alamu na dacen mijin aure kamin mace ta amince da mai sonta da aure, ga Karin wasu alamomin da suke tabbatar miki da kinyi dacen mijin aure:

 

1: Namijin daya damu da damuwarki.


2: Namijin da kullum sai ya kiraki ya tambayeki yadda kika kwana, kika wuni da kuma yi miki fatan tashi lafiya.


3: Namijin Da Yake Baki Lokaci Baya fakewa da aiki yayi masa yawa.


4: Namijin da yake sauraronki yake baki hankalinsa a duk lokacin da kike son zantawa dashi na muhimmi.


 

5: Namijin da baya jira har sai kin tambayeshi.


6: Namiji mai cika alkawari. Duk alkawarin da ya miki yana kokarin ya cika. Bana naki kadai ba har na wasu daban. Wannan ba mijin yadawa bane, rike shi gam.


7: Namiji mai furta miki kalaman so a fili, a baka da kuma kuna ku biyu.


8: Namiji mai kalamai masu kyau a lokacin farin ciki da kuma bacin ransa.


9: Namijin da yake da zumudin bashi dama yaga iyayenki ko magabatanki.


10: Namiji mai nuna miki farin cikinsa da kuma yi miki godiya a duk lokacinda kika yi abun ayaba miki. Da kallon kwalliyarki ya yaba. Idan kin kawo masa ruwa ko abinci ya jisu daban da wadanda ya saba.


11: Namiji mai amafni da wadannan kalmomin guda biyu, magiya idan zai saki masa wani abun. Ya kuma ce ya gode idan kika masa, (please and thank you).


12: Namijin da baya kunyar a ganki da shi.


 

Da fatan mata zasu kula da wadannan abubuwan ba su maida hankali akan aljihunsa ko abar hawansa ba.

Comments