Min menu

Pages

Wasu yankuna da mata suke rige rigen samun saurayi saboda yadda suke da yawa.

 Wasu yankuna da mata suke rige rigen samun saurayi saboda yadda suke da yawa.Akwai yankuna da mata keda matukar yawa harma yawansu ya nunka na maza da kaso mafi tsoka, wannan yasa matan ke shan wahala sosai a wajen samun abokin rayuwa.


An bayyana yadda matan ke rige rigen samun saurayi a wadannan guraren, duk yarinyar da tai dacen samun saurayi to da wuya ta bari wannan saurayin ya kufce mata.


Yan mata a wadannan guraren suna iya bakin kokarin su domin ganin samarinsu da suke a tare basu barsu ba.


Idan yarinya ta samu wanda yake sonta to kuwa za kuga hankalinta ya kwanta kuma zata tsaya kaida fata dan ganin wannan saurayin bai rabu da ita ba.


Kai tsaye muje ga jerin wadannan kasashen ko kuma yankunan.


1 Nepal :- Bincike ya nuna wannan yankin yafi ko ina yawan mata domin sunada wajen kaso 55 na yawan mata wannan yasa yan matan yankin suke rike samarinsu kankam.


2 Ukraine kowa yasan mata a kasar Ukraine sunfi maza yawa wannan yasa samari sukai karanci duk budurwar da tai dacen saurayi bata yadda wani abu ya hadasu har su rabu.


3 Russia Kasar Russia itama kasa ce da maza suka fi yawa wannan yasa samun samari gurin yan mata yake da wuya a wannan yankin.


4 Latvia :- Idan yarinya ta samu saurayi a wannan yankin to bata yadda su rabu saboda yadda maza ke wahalar samu.


Bincike ya nuna matan yankin yawansu yafi na maza sosai da sosai.


5 Portugal :- Mata a kasar Portugal suna da yawan gaske wannan yasa samari ke wahalar samu a gun yan matan kasar.Comments