Min menu

Pages

Video: Kabilar Da Ake Bawa Budurwa Alade 10 Amatsayin Dukiyar Aure

Dani Tribe Village

Kabilar Da Ake Bawa Budurwa Alade 10 Amatsayin Dukiyar Aure

Masu iya karin magana suna cewa 'Allah daya garin bam bam' domin kuwa wannan magana gaskiya ce, a irin binciken da muke domin kawo muku abubuwan mamaki da suke faruwa a wannan duniya wannan karon mun samo wani labari da kuma video na wata kabila da idan zaka Auri Budurwa sai kasayi Aladu 10 zuwa 20 a matsayin sadakin aurenta

Kamar yadda muka sani cewa anan arewacin Nigeria idan mutum zai auri mace to dole zai saya mata kayan sakawa da kuma uwa uba Sadaki, sai dai su wannan kabila abin ba haka yake ba agarinsu, domin kuwa idan kana son mallakar mace a matsayin matar aure dole sai kanemi Alade 10 ko 20 ya danganta da kyawun matar da kuma darajarta kuma wadannan Aladu sune dukiyar aurenta,

Kasan Menene Alade? 

Alade wata dabba ce mummuna kuma a musulunci ma haram ne cinta, amma wadannan mutane alamu yanuna cewa Alade dabba ce mai daraja da kima uwa uba kuma ga Tsada idan kaje kasuwa domin sayanta, kuma wannan kabila basa saka tufafi kamar yadda sauran mutane suke sakawa kawai dai suna kare al'aurar sune da wani abu wanda za iya cewa kawai Tsirara suke yawo

Wannan Kabila ana kiransu da Dani ko kuma Dani Tribe Village kamar yadda wata kungiya take kiranta wanda tasamu zuwa har inda wadannan mutane suke rayuwa domin nunwa duniya Al'adar wannan kabila, mun samo muku Video yadda Kabilar Dani suke rayuwa zaku iya kallon videon akarshen wannan rubutu


Comments