Min menu

Pages

Wani gari wanda mata kadai ne ke rayuwa a ciki.

 Wani gari wanda mata kadai ne ke rayuwa a ciki.



Kamar yadda muka taso haka muka ga ana yi wato duk wata kasa,wani birni ko kuma wani gari ko kauye za aga mata da maza ne ke rayuwa a ciki kuma suke gabatar da al'amuransu na yau da kullum.


Kowa ya riga yayi ammanna da cewar jinsi daya bazai iya rayuwa ba tare da taimakon daya jinsin ba, ina nufin jinsin maza baza su taba rayuwa ba tare da mata a kusa dasu ba haka ma maza.


To saidai ana haka mukai kicibis da wani gari da ya bada mamaki kuma ya wanzu tsawon lokaci inda mata ne kadai suke rayuwa a wannan garin ba tare da maza ba wannan kuwa ya faru ne saboda wasu dalilai da suka faru ga matan dake cikin wannan garin.


Umoja yankine a arewacin kenya, tsawon shekaru masu yawa da suka shude. Mutanen Samburu suna bin rayuwarsu ta asali wanda suka gada tun iyaye da kakanni.

hakan ya samo asali ne daga wata mata da ake kira Rebbeca lolosoli ita ta kafa ƙauyen Umoja shekara talatin da suka wuce ta kafa wannan kauye ne saboda ba mata kariya, saboda yawaitar fyaɗen da ya faru har yara mata goma sha biyar sojojin british sukai ma fyaɗe a shekarar 1990, in da a yau garin ya zama mafaka ga duk wata ƴa mace da ke wannan yanki, na guje ma fyaɗe, ko auren dole, ko wani abu da maza ka iya cutar da su, matuƙar kika shiga wannan ƙauye kin tsira. shiyasa ƙauyen na Umoja ya ci sunan shi na zaman lafiya ga mata.


ƙauyen dai tamkar ƙauyen samun cikakken ƴanci ne ga mata, in da Mata kawai aka yarje su shiga wannan ƙauyen ba tare da wani matsala ba domin suje su rayu cikin kwanciyar hankali.

Idan  wani namiji zai shiga wannan ƙauyen sai ya biya, kuma ba'a amince ya kwana ba koya tsaya bata lokaci.

 Sannan tsofaffin da suke garin suna koyama mata sana'o'i irin na zamani kama daga warwaro, abun wuya abun hannu, da duk wasu dabaru da zasu dogara da kansu, sannan kuma ana koyamusu yadda zasu kare kansu daga haɗarin maza, sukan ɗauki kayan su da suka haɗa sukai makotan garinsu su dunga siyarwa.


A takaice dai babu wasu mazan da suke rayuwa a wannan garin face mata kuma kusan duk wacce ta kawo kanta wannan garin to zaka samu ta gujewa wani al'amari ne dake tunkaro ta kodai domin ta kare kanta ne daga farmakin da maza ke son kawo mata ko kuma ta gujewa auren dole ne.

Tun garin yana dan kadan harya kasance mata sun fara taruwa da yawa.

Matan dake wannan garin suna zaune cikin kwanciyar hankali.


To jama'a mu kasance tare daku a wani sabon shirin.

Comments