Min menu

Pages

Kabilar da suka fi dadewa a Nigeria

Kabilar da suka fi dadewa a Nigeria
Nigeria kasa ce dake da tarin jama'a wanda mutanen dake rayuwa cikinta sun haura mutum miliyan ashirin, sannan kasar tana daya daga cikin manya kuma jibga jibgan kasashen dake cikin nahiyar Africa baki daya.

Kasar tana iyaka da wasu kasashen kamar Benin, Niger, Cameron da kuma Chad.
Akwai manyan tsaunuka da koguna tare da koramu da kwazazzabai a kasar wannan yasa aka samu kasar noma da kuma albarkatun kasa masu tarin yawa dangin su zinare lu'u lu'u, jauhari man fetir da dai sauran abubuwa.
Kasar ta kasance kasa wacce ta kasance tsohuwa ko kuma muce dadaddiya hakan yasa aka samu kabilu wanda suma suka dade tun kafuwar wannan kasar.

To yau cikin shirinmu zamu fada muku wasu daga cikin kabilu mafiya dadewa tun kafuwar wannan kasar.
Kafin muje cikin shirin ku taimaka ku danna mana subscribe da like idan a youtube kuke kallo sannan kuyi following din wannan Page din namu idan a Facebook kuke biye damu wannan zai 
bada dama daga zarar mun dora abu kuna gani.

Kabilar Igbo:- Bincike ya nuna kabilar Igbo ita ce kabila ta farko kuma kabila tsohuwa wacce ta wanzu tun wani karni daya shude kuma ta zamto kabila mafi dadewa a kasar Nigeria. 

Kabilar hausa:- Kabilar hausa bincike ya nuna sune kabilar ta biyu mafi tsufa ko kuma mafi dadewa a Nigeria kabila ce mai dadadden tarihi wanda ta wanzu tun karni mai tsawo a baya.

Kamar yadda mutane suke fada kabilar ta kafu ne tun zuwan wani dan sarki daga cikin sarakunan kasar Iraq wanda ake ce masa bayajidda wanda ya sauka a garin daura.

Wannan yasa yaren kabilar hausa ta kasance daga cikin kabilu mafiya dadewa a Nigeria.

Yoruba:- Kabilar Yoruba ta zamto ta uku daga cikin kabilun da suka kasance tsofi kuma mafiya dadewa a Nigeria domin kabilar ta kasance ta kafu tun shekaru daruruwa da suka wuce.
Masu bincike sun nuna cewar kabilar ta kafu ne daga gurin Oduduwa.

Bayan wadannan akwai wasu kabilun da suka dade kamar fulani da kuma kabilar agbo to saidai kamar kabilar fulani bata kai sauran kabilun dadewa ba.


Comments