Min menu

Pages

WATA ƘABILA A KUDANCIN NIGERIA WANDA BASA AUREN SIRIRIYAR MACE SAI LUKUTA

WATA ƘABILA A KUDANCIN NIGERIA WANDA BASA AUREN SIRIRIYAR MACE  SAI LUKUTA
Kun san kowacce ƙabila da irin al'adun su da suke gabatarwa lokacin bukukuwar auren su, to kamar hakane ya kasance ga wata ƙabila mai suna EFIK da kuma  inda su yarinya ba zatayi aure ba har sai tayi ƙiba ta zama lukuta.

Kabilar suna nan a jihar Cross rivers da kuma wani bangare na kasar West Africa

 Dan haka yan kabilar suka samu wani guri suka ware musamman domin suke gabatar da tsaface-tsafacen su, a gurin an ware wasu mabanbantan ɗakuna da ake saka ko wacce yarinya da ta tashi yin aure. 


Matuƙar yarinya ta isa aure mahaifin ta zai ɗauke ta ya kaita wannan guri ya biya duk wani abu da ake buƙata na kula da ita don a killace ta a cikin wannan ɗakin hakan zai nuna lallai iyayen yarinya suna so su aurar da ƴar su, idan har aka saka yarinya a wannan ɗakin ba wanda zai dunga zuwa gurin yarinyar  kama daga ƴan uwanta, ƙawayen ta da duk ƴan gari, sai wasu dattawa da manyan gari ake  warewa wanda zasu dunga zuwa suna kula da yarinyar, suna bata abinci suna koyamata yadda ake zamantakewar aure, sannan zasu dunga mata duk wani nau'i na gyaran amarya gurin anfani da abubuwa gyara na itatuwa da sauran na'un irin su mai da ake samu daga itatuwa, sannan za'a aske ma yarinya kan ta zakuma a ɗaura mata wani kambu a wuyar ƙafarta, haka za tayi ta zama a wannan ɗaki suna gabatar mata da duk wani abubuwan al'ada har tsawon wasu watanni kafin aure.


 Lokacin da aka fito da Amarya zaka ganta tayi ƙatuwa, tayi kyau saboda gyara da da cin abubuwa na ƙara girma.


Daga nan sai a fara shirye-shiryen aure.


Mu kasance daku a wani sabon shirin

Comments