Min menu

Pages

Gine ginen da suka fi kowanne gini tsawo a Duniya baki daya.

 Gine ginen da suka fi kowanne gini tsawo a Duniya baki daya.



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya aiki ya fama ya kuma hakurin kasancewa tare damu?


Hakika muna jin dadin yadda kuke tare damu koda wanne lokaci.


Idan da gyara ko bada shawara ku fada mana domin mu gyara wannan shine zai bada damar mu gane kuna tare damu koda yaushe.


Yau cikin shirin namu munzo muku ne da jerin wasu gine gine wanda suka fi ko wanne gini tsawo a Duniya.


Akwai gine gine masu tsawo na ban mamaki, wanda idan mutum yai karo dasu zai cika da al'ajabi har wani ma yana tunanin ta yadda akai aka iya gini mai tsawo na ban mamaki haka, wasu ma gani suke babu yadda za ai mutane su iya yin irin wannan ginin saidai ko aljanu.


Burj khalifa dake Dubai:- Bincike ya nuna a fadin duniya babu wani gini da yakai tsawon wannan ginin na Burj khalifa dake Dubai, domin an nuna tsawonsa yakai kamu dubu biyu da dari bakwai da goma sha bakwai.


Da Burj Dubai ake ce masa kafin daga baya a mayarda sunansa Burj khalifa domin girmama sarkin.


Akwai office office cikin wannan ginin na Burj khalifa Dubai da kuma bangarori mabanbanta.


Shanghai Tower yazo na biyu cikin jerin gine gine masu tsawo a Duniya domin yakai tsawon kamu dubu biyu da sabai'in da uku, an raba wannan ginin bangare tara wanda aka ware office office da kuma sauran gurare.


Dogon gini mai dauke da agogo dake makka:- Bincike ya nuna guri na uku da yafi tsawo a duniya bangaren gine gine shine ginin dake makka wanda ke dauke da agogo na alfarma da ake cewa royal clock duk wasu da suka ziyarci gurin sunga yadda ginin yake.


Akwai gine gine kamar bangaren gwamnatin kasar da kuma inda bakin da suke zuwa kasar ibada suke sauka sannan an bayyana wannan gurin a matsayin guri mafi tsada da kudinsa yakai kimanin dollar billion goma sha biyar.


Wadannan sune gine gine mafiya tsayi a duniya yanzu, duk da akwai sauran guda biyu da bamu ambata ba amma su tsawonsu basu kai wadannan da muka ambata dayar a Shanghai take itama ana ce mata ping an finance tower dayar kuma a South Korea take ana kiran wajen da suna Lotte world tower.


Mu kasance tare daku a wani sabon shirin.

Comments