Min menu

Pages

Pi Network Karyane Amma Ba Damfara Bane - Dalilai 3 Daga Masana Crypto Currency

Pi Network Karyane Amma Ba Damfara Bane

Yanzu muna zamanin da mutane suke samun arziki ta hanyar Digital Currency wato kudaden internet irin su Bitcoin da kuma sauran coins masu kama dashi, 

Pi Network wani sabon kudin internet ne ko kuma ace yana gab da zama kudin internet wanda mutane dadama suka dora fata da burin samun makuden kudade akansa

Wata fargaba shine masana dayawa sun soki tsarin Pi Network da kuma ikirarin su na cewa coin din nan gaba zai zama mai daraja sosai, sai dai akasari basa kiransa da Damfara (Scam) amma suna ganin Pi Network Karyane

Menene Pi Network?

Pi Network wani sabon kudin internet ne (digital currency) wanda ake kokarin sanyashi a jerin manyan kudaden internet kamar Bitcoin da Ethereum sai dai kamar yadda muka fada a baya har yanzu Pi Network bashi da wata daraja saboda ba a saka shi a kasuwar coin ba

Minepi.com website yayi alkawarin cewa za a yi launching din Pi a farkon wata disamba na wannan shekara, sai dai har yanzu hakan bata tabbata ba kuma kuma basu fadi dalilin rashin launching din ba

Yaya Ake Amfani Da Pi Network?

Abune mai sauki idan kana son fara samun Pi Network kuma wani abin burgewa shine kyauta ne baka bukatar kashe ko Naira daya, sai dai a kullum zaka je kayi dan karamin aiki (Mine) domin tara pi coins.

Zaka iya samun manhajar Pi Network akan Playstore idan kana son fara samun kudin Pi Network, idan kayi download na app din zakaga inda zakayi rigista da phone number ko kuma Facebook account daga nan zaka iya fara Pi Mining nan take

Pi Network Karyane Amma Ba Damfara Bane - Dalilai 3 Daga Masana

Hausawa sunce "Wani hanzari ba gudu ba" shine duk wani kasuwancin internet ko kuma wata hanya da wani zai kawo ta online business akwai kalubale acikinta,

Masana harkar Crypto Currency sunyi nazarin Pi kuma sun bayyana ra'ayinsu akansa, akasarin abin da suke cewa shine Pi Network karyane kuma mun nemo dalilai 3 da suke tabbatar da hakan

Dalili Na 1 - Amfani Da Ads

Wani nazari da akayi shine Pi application yana amfani da talla (Ads) wanda hakan yana nuna suna samun kudi ko kuma ace suna karuwa da mutanen da suke shiga kullum da wannan tallan

Duk wanda yasan tsarin Google Admob yasan cewa Google yana saka talla akan application kuma adadin wanda suka kalli tallan yawan kudin da mutum zai samu

Don haka masana suna ganin ana yaudarar mutane ne suna shiga da sunan Mining Pi amma kuma masu abin suna amfani da sune domin samun kudin talla

Dalili Na 2 - Rashin Launching Dinsa

Wani abin dubawa shine akwai kananan digital currency da aka kaddamar dasu wanda basu kai Pi yawan mutane ba ko kuma ace ko rabinsa basu kai ba, amma yanzu haka suna cikin jerin coin din da suke Blockchain

A watan September 2021 kamfanin Pi ya sanar da cewa suna da  mutane 25Millions wanda hakan ba karamar nasaba bace ga masu abin,

Idan aka duba yawan mutane yakai ace yanzu Pi ya shiga kasuwar Crypto kuma ansan darajar sa, sai dai har yanzu ba alamun hakan

Dalili Na 3 - Rashin Cika Alkawari

Duk wani mai yin Mining Pi yasan cewa kamfanin yatabbatar da cewa karshen wannan shekara 2021 cikin watan disamba zai ayi launching dinsa kuma za fadi darajarsa a kasuwar Crypto Currency.

Sai dai watan yashiga babu labari kuma basu fadi wata rana guda wacce zasu yi hakan ba, idan sun samu wata matsala ce yakamata su sanar da masu amfani dashi saboda su kara musu karin gwaiwa

Pi Network Ba Damfara Bane

Sai dai duk masu wannan nazari basa cewa Pi Network Scam ne duk da sun ce karyane, dalilin su na cewa ba damfara bane shine babu wani kudi da mutum zai kashe domin amfani dashi

Idan aka dauke lokaci da mutum zai bata da kuma bayanai (Data) da kamfanin zai iya dauka babu wani abu daza karasa don kana amfani da Pi

Note: Wannan sharhi munyi shine gwargwadon abin da muka bincika a Internet daga masana harkar Crypto Currency da kuma masu nazari akan kasuwancin Internet

Don haka idan kaga wani kuskure zaka iya bamu shawara.



Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment