Min menu

Pages

Kabilar da mata ke auren bishiya maimakon su auri mutane maza

 Kabilar da mata ke auren bishiya maimakon su auri mutane mazaAkwai abin takaici sosai idan idanuwan mutum sukai karo da wasu jama'ar mutane masu aikata wasu abubuwa a bayan kasa.


Mutum yakan rasa abinda zaiyi tsakanin mamaki ko kuma rashinsa idan yaga wasu sun aikata wani abin.


Domin wani gani zaiyi abinda wannan al'ummar suke aikatawa bashi da maraba da hauka ko rashin hankali.


Idan aka ce za'a baku labarin Duniya da kabilun cikinta da yadda wasu mutanen suke rayuwarsu tare da gabatar da abubuwan su, wasu zasu dauka karya ne domin za suji abinne wani iri haka kamar ba'a duniyar bane ake gabatar da hakan.


Kamar gurinda suke kone duka matar da mijinta ya mutu ya barta.

Ko kuma gurinda sai mutum yayi tafiya akan garwashin wuta idan matarsa tanada ciki.


Ko kuma garinda suke fitar da mata daga gari da zarar suna da juna biyu.


Da dai sauran abubuwa masu ban mamaki gamida al'ajabi.


Yau ma cikin shirin namu munzo muku ne da labarin wani wata alkarya dake kasar India inda mata suke auren bishiya.


Abin da takaici ace mutum dan Adam amma ya rasa me zai aura sai itace ko kuma tsiro.


Akwai wani abu da yan abu da yan yankin suke kira Manglik. Wata al'ada ce da suke gabatarwa a wani yanki na kasar India shine mace nada damar da zata auri duk abinda taga dama kamar ta auri dabba irinsu kare ko kuma su auri bishiya da dai sauran abinda suka ga dama.


Kamar kabilar santhal sunyi amanna da cewa idan suka haifi yaro yakai lokacin fitar da hakori to akwai matsala dan haka suke fara auren kare tukunna wanda duk wacce tayi wannan auren to daga karshe koda ta auri mutum babu abinda zai sameta koda haihuwa nawa za tayi.


Hakama akwai wata kabila da daga zarar yarinya ta fara girma har ta fuskanci ta fara fitar da jinin al'ada to zatai sauri ta auri ayaba ko kuma ta auri kare.


Sannan ba iya kasar India ne ke gabatar da irin wannan abinda harda sauran wasu kasashen saidai dalilin kowa yasha banban dana dana dan uwansa.


Mu kasance a wani shirin.

Comments