Min menu

Pages

Kabilar da suke rayuwa a RUWA

 Kabilar da suke rayuwa a RUWAAbubuwan mamaki dai da wuya su kare a duniya, sannan duk mutumin da yake zagayawa cikin duniya dole yayi karo da abubuwa na mamaki wasu su baka tsoro wasu su baka tausayi yayinda wasu ma haushi da takaici zasu bewa mutum.A yau cikin shirinmu muna tafiya ne da sunan wata kabila mai suna BAJAU wanda su basu da wani guri da suke rayuwarsu daya wuce ruwa.


Basu iya zama akan kasa ba saidai cikin ruwa  a cikinsa suke gabatar da komai nasu kama daga gidansu, gurin zamansu dadai sauran abubuwan da suke yau da kullum.


Kabilar BAJAU suna karar da duk wata rayuwarsu ne a cikin ruwa, anan suke haihuwa yayan su girma, basu da gun yawo sai cikin kwale kwale. Sannan sunyi amanna da cewar rayuwarsu zata wanzu ne kawai idan suna cikin ruwan domin baza su iya rayuwa akan doron kasa ba kamar yadda sauran mutane suke rayuwa.


Comments