Min menu

Pages

Jerin mata guda goma mafiya arziki a nahiyar afirka a shekarar 2021

 Jerin mata guda goma mafiya arziki a nahiyar afirka a shekarar 2021



Shekaru da yawa abaya an dauki mata a matsayin kawai zama a gida,kula da yaransu da kuma sauran aikace-aikacen gida.


Amma ayau mata sun zama gagara badau a kowane fanni na rayuwa,kama daga kan kasuwanci,shugabanci da sauran gudunmowowi da mata ke bayarwa a zamantakewa da rayuwa.


Yanzu ga wasu daga cikin mata guda goma a afirka mafiya arziki.


Wadannan mata sun tara dukiya me tarin yawa,sannan suna jagorancin mutane da yawa a wasu bangarori na rayuwa masu tarin yawa.


Bugu da kari,abune me kyau musansu saboda sun cika burika da yawa a rayuwarsu.


Bari mu tafi kai tsaye zuwa ga sunayensu,kasar da suke da kuma adadin kudinbda suka mallaka.


1. Isabel Dos Santos



Kasa: Angola


Sunan kamfani: Zon Multimedia


Adadin kudi: Dala biliyan 2.2 [$2.2 billions]


A lokacin da mahaifinta yake kan mulkin kasar ta angola ne ta zama head of sonangol (wani bangaren kula da harkon man kasar)


An nadata ne akan wannan mukamin a shekarar 2016,amma kuma an sauke ta daga bisani bayan sabon shugaban kasar ya karbi mulki a shekarar 2017.


Tana da kudin daya kai kimanin dala biliyan 2 da miliyan dari biyu,ta kasance mace ta farko mafi kudi afirka.


2. Folorunsho Alakija



Kasa: Najeriya


Sunan kamfani: Rose Of Sharon Group


Ita kuma folorunsho ta kasance ‘yar kasuwa wadda take jan hankalin kwastomominta kamar irinsu matar ibrahim badamasi babangida a lokacin mulkinsa na shugabancin kasa da kuma sauran manyan mutanen kasar ta najeriya.


Sannan ta mallaki kudin daya kai dalar amurka biliyan daya da miliyan dari ($1.1 billions)


3. Ngina Kenyatta



Kasa: Kenya


Sunan kamfani: CBA


Adadin kudi: Dala biliyan daya ($1 billion)


Ngina kenyatta ta kasance hamshakiyar yar kasuwa kuma me kirkirar sabon abu,an haifeta a shekarar 1933 a kasar kenya.


Amma a shekarar 1951 ta auri jomo kenyatta 


Sannan mijin nata ya zama shugaban kasar kenya sannan ya rasu a shekarar 1978


Ta kasance matar jomo ta hudu kuma an bayar da ita kyauta ne gashi jomo din daga kabilar su.


Wannan ne yasa ake mata lakabi da ‘uwa ga al’umma’


Kafin mutuwar mijin Ngina ta haifi ‘ya ‘ya guda hudu gashi jomo kenyatta.


Ayau Ngina kenyatta itace uwar shugaban kasar me suna Uhuru kenyatta (da ga shi jomo)


Gaba daya acikin shekarun ta mallaki plantations,ranches,hotels,company da sauransu.


Yanzu haka tana da kudin daya kai kimamin dalar amurka biliyan daya $1 billion.


4. Divine Ndhlukula



Kasa: Kenya


Sunan kamfani: SECURICO


Adadin kudi: Dala miliyan dari takwas da tara $809 millions


Divine Ndhlukula ta kasance ‘yar kasar zimbabwe kuma ‘yar kasuwa wadda ta mallaki kamfanin tsaro me suna SECURICO.


Bugu da kari,ta karbi takardar karatun digiri daga jami’ar Midlands University,sannan daga bisani ta karbi takardar MBA a jami’ar mata University of Africa.


Sannan tayi PhD a fannin kasuwanci duk a jami’ar.


Divine ta fara aiki ne a babban kamfanin sadarwa kafin ta zama akawu a kamfanin Old Mutual.


Bayan nan itace ta samar da daya daga cikin babban kamfanonin tsaro a kasar ta Zimbabwe.


Kuma itama ta mallaki kudin daya kai dalar amurka miliyan dari takwas da tara $809,wannan yasa ta zama ta hudu a jerin mata masu kudin afirka.


5. Bola Shagaya



Kasa: Najeriya


Sunan kamfani: Bolmus Group International


Adadin kudi: Dala miliyan dari shida da talatin $630 Millions


An haifeta a shekarar 1959,bola shagaya ta kasance gagarumar ‘yar kasuwa wadda take ta hudu a jerin mata masu kudin afirka.


Kafin ta zama yar kasuwa a shekarar, 1983 tayi aiki a matsayin audit a wani bangare na babban bankin najeriya.


Ta fara kasuwanci ne ta hanyar shigo da kayayyakin daukar hoto.


Yanzu haka tana da brand nata na kanta na photography me suna Konica.


Ayau itace darekta ta practoil ltd.


Wannan kamfanin nata na daya daga cikin manyan kamfanonin shigo da mai da bakin mai a najeriya.


Yanzu haka ta auri Alhaji Shagaya (mamallakin babban kamfanin sufuri a najeriya) kuma tana da ya ya shida.


Bola ta mallaki dalar amurka miliyan dari shida da talatin.



6. Wendy Appelbaum



Kasa: South Africa


Sunan kamfani: Pick N Pay Holdings Ltd


Adadin kudi: Dala miliyan dari da casa‘in


Wendy yar kasuwa ce wadda aka haifeta a babban birnin South Africa (Cape town).


Bayan kammala karatunta a kwaleji,tayi digiri a jami’ar ta cape town.


Yanzu haka itace darakta ta kamfanin Pick N Pay Holdings Ltd.


Kamfanin ya kasance me gidanta ne yasaya me suna Raymond.


Suna aiki tare domin habaka ko tafiyar da kamfanin.


Baya ga kasuwancin nata,ta kasance haryanzu me taimakawa mutane.


Ta zamto mace mafi kudi a kasar ta South Africa ayau.


Ta mallaki dalar amurka dari biyu da hamsin da tara,hakan yasa ta zama ta shida a jerin matan masu kudin afirka.


7. Wendy Ackerman



Kasa: South Africa


Sunan kamfani: ETF


Adadin kudi: Dala miliyan dari da casa‘in $190.2 million


Itama an haifeta a kasar ta south Africa kuma itace ta samar da Education trust fund.


Wannan wani matakine na tallafawa yara dalibai musamman marasa galihu domin cigaba da karatunsu.


Wendy itace ta bakwai,wadda ta mallaki dalar amurka miliyan dari da casa’in.$190.2 million.


8. Irene Charnley



Kasa: South Africa


Sunan kamfani: Smile Telecom


Adadin kudi: Dala miliyan dari da hamsin. $150 million


Irene yar kasar South Africa ta kasance yar kasuwa wadda aka haifeta a shekarar 1960.


Tana daya daga cikin kungiyar kasuwancin South Africa.



Bayan ta bar kungiyar ne ta koma cikin kamfanin sadarwa,wadda daga bisani ta zama darakta a kamfinin sadarwa na MTN.


Wannan kamfanin shinnle babban kamfanin sadarwa a daukacin afirka.


Sannan ta taimaka wajen yada kamfanin na MTN zuwa wasu kasashe.


Yanzu haka ita ta mallaki kamfanin Smile Telecom Holdings Ltd.


Harwayau dai kamfanin yana aiki a wasu kasashen afirka da suka hada da Najeriya,Uganda da sauransu.


Yanzu haka tanada kudin daya kai dalar amurka miligan dari da hamsin.


9. Bridgette Motsepe Radebe



Kasa: South Africa


Sunan kamfani: Mmkau Mining


Adadin kudi : Dala miliyan dari.$100 million


An haifeta a shekarar 1960,yar kasuwa kuma kuma shugaba a kamfanin SAMDAU.


Yana daya daga cikin kamfanonin sarrafa ma’adanai a kasar ta south Africa.


Shekaru baya ta fara wannan kasuwancin na hakar ma’adanai kafin ta kafa kamfani.


Wannan ya taimaka wajen fitarwa,ganowa da kuma sarrafa ma’adanan gwal da kurom da platinum.



Yanzu haka ta mallaki dalar amurka miliyan dari,kuma daya daga cikin masu kudin afirka na mata.


10. Sharon Wapnick



Kasa: South Africa


Sunan kamfani: Octodec Investment


Adadin kudi: Dala miliyan arba’in da uku.$43.2 million


Sharon wapnick yar kasar South Africa kuma yar kasuwa wadda ta gaji kamfanin mahaifinta me suna Octodec Investment da kuma dukiyoyin masu tsada bayan mutuwarsa.


Baya ga gadar dukiyar nahaifin nata sharon ta kasance daya daga cikin masu zartar da doka wadda ake kira TWB Attorneys.


Ta kuma kasance yar kasuwa hamshakiya kuma me kudi a kasar ta south Africa dama afirka baki daya.



A karshe wadannan sune jerin sunayen mata goma mafiya kudi a nahiyar afirka tareda takaitaccen tarihinsu,kasar da suke,sana’o’in da suke da kuma adadin kudin da suka mallaka.

Comments