Min menu

Pages

Wakar da Sarah Aloysius Stephanie tayiwa Manzon Allah

 Wakar da Sarah Aloysius  Stephanie tayiwa Manzon AllahJarumar kannywood din da take taka rawa a cikin wani shiri mai dogon zango mai suna dadin kowa wato Sarah Aloysius wacce akafi sani da Stephanie ta fitar da wata kasida wato bege wacce tayiwa ma'aiki duk da kasancewar ta ba musulma bace.

Idan kuka duba kasa mun ajiye muku wakar da tayi

Sarah Aloysius din wato Stephanie tace tsananin kaunar da taga musulmi na yiwa annabinsu yasa tayi wannan begen.


Tuni dai mutane sun fara maganganu akan begen da jarumar fina-finan hausa tayi har wasu daga ciki suka fara addu'a suna neman ta musulunta.


Wani ma dai yayi karin haske ga wakar da Stephanie din tayi wato yar kabila sunan wani shiri mai dogon zango da take shiryawa.


Ga abinda yace a game da wakar ta Stephanie


Ga Karin wakar Yar uwa Sarah Stephanie Ga ma'aikin Allah s a w tare da fasara shi zuwa harshen Hausa


(1) Assalamu'alaika Habib yah rasulullah*


(2)Assalamualaika Habibi yah Nabiyallah**


Fasarar wanan baiti shine Amincin Allah yatabbata gareka ya masoyin Allah s w 


Amincin Allah yatabbata gareka yha manzon Allah s a 


Sharhi***********Dafarko dai Sarah ba musulma bace kamar yadda tayi bayani a idon duniya kancewa soyayyar da musulmai ke nunawa ne ga manzon Allah s a w yasa ta itama nuna soyayya gareshi harda rera masa Yabo da wasu kalmomin Larabc


Abu nabiyu shine Sarah tayarda annabin mu annabi Muhammad s a w masoyin Allah ne s w a kuma dan gatane nagaban goshi ne acikin halittun Allah ga yadda tafahimci martaba da kuma matsayinsa a wajen Al'ummar musulm


Abun na uku shine dakanta Sarah ta amince shi manzon Allah ne kuma dan sakone na Allah izuwa ga mutane da Aljanu da dukan mai motsawa da Mara motsawa  jama'ar musulmi wanan yana daga cikin nasara ta musulunci sanan kuma daga cikin kyawawan dabi'u irin na rasulullahi shine riko da gaskiya da amana kyautatawa Wanda ba Adinin Ku dayaba ma yana daga koyarwan manzon Allah s a w


Jama'a musulmi wanan wata nasarace danake kallo take tunkaro musulmai dalilin kyakkyawar mu'amala da Wanda ba musilmi ba saboda HK inakiran mu da muhada kanmu babu wariyar aqeeda a musulunci domin ranar lahira Allah musulunci kawai zai tambaye mu akai ba aqeedun mu ba


Ina mai tunatar damu yan uwa musulmai kada mufifita aqeedar mu sama da Adinin mu domin gujewa fadawa halaka Allah kahada kan musulunci da musulmai  kabar mu da kaunar  Annabi Muhammad s a wa. .


Ga wakar da Stephanie din tayi

Ku danna nan

Nan


Comments