Min menu

Pages

Rabiu Musa kwankwaso yau yake cika shekaru 65 da haihuwa, Wani abu da ya kamata matasa su koya a game da rayuwar wannan dan siyasar

 Rabiu Musa kwankwaso yau yake cika shekaru 65 da haihuwa, Wani abu da ya kamata matasa su koya a game da rayuwar wannan dan siyasar
Yau Alhamis, 21 ga watan Octoba, 2021.

Mai girma tsohon gwamnan Jihar Kano, Madugun ɗarikar siyasar Kwankwasiyya ƙarƙashin jam'iyyar PDP, Eng. Rabi'u Musa Kwankwaso ya cika shekaru 65 a wannan rana.


Ba shakka shekaru sun yi albarka, domin duniya ta shaida ko da za a ƙi Kwankwaso a saboda bambancin siyasa, to dole a yarda ya shimfiɗa ɗumbin ayyukan alkhairan da za a daɗe ana amfana a Jihar Kano da Arewa da ma Nageriya gabaɗaya.


Babban alkhairin da Kwankwaso ya dasa wanda zai cigaba da girma da yaɗo ana amfana shi ne: dashen al'umma kuma matasa. Shakka babu Kwankwaso ya dasa ɗan adam, ya gina matasa sun samu ilimi da maciyar abinci. A yau ɗumbin matasa Malaman Jami'a da manyan makarantun gaba da sakandire da likitoci da haziƙan matasa da ke tasowa a fannoni daban-daban na rayuwa kusan duk dashensa ne, ana kuma amfana da su.


Bayan dasa ɗan adam, a gwamna da ya yi tsawon shekaru takwas, ya kuma shimfiɗa tituna, in ka ɗauke Malam Ibrahim Shekarau, kusan Kwankwaso shi ne gwamnan da ya samar da mafi yawan hanyoyin mota da ake bi a yau. Ya yi gwamna cikin izza ba sani ba sabo, ya kuma shimfiɗa ayyukan raya ƙasa da dama, har yau duk gwamnan da ya zo a kansu ya ke ɗorawa.


Haƙiƙa Kwankwaso mutum ne, kuma ɗan siyasa ne na gaske, kowa zai so ace ya na da jagora irinsa saboda sadaukarwarsa wajen gina mutane. Da ace Arewa ta na da irin Kwankwaso biyar ba shakka da cigabanmu ya wuce yadda mu ke a yau. Na kuma tabbata a kwai buƙatar ace mun sanya ɗamba kowane matashi mai tasowa ya yi ƙoƙarin zama Kwankwaso, ma'ana idan ya samu dama ya yi amfani da ita wajen ba wa wasu dama.


Ina taya Kwankwaso murnar cika waɗannan shekaru ɗaiɗai har guda 65, Allah ƙara masa lafiya da imani da nisan kwana masu albarka. Comments