Min menu

Pages

KAMFANIN FACEBOOK, WHATSAPP DA INSTAGRAM YA HADU DA MUMMUNAN HARI

 KAMFANIN FACEBOOK, WHATSAPP DA INSTAGRAM YA HADU DA MUMMUNAN HARIJiya Litinin da yammaci gungun hackers sun samu nasaran yin hacking din kamfanin facebook, WhatsApp f Instagram wanda hakan yasa kamfanin ya sauke Server dinsa, dalilin da yasa kenan suka dena aiki a lokaci guda tsawon awanni 6, kasancewar duka kamfani daya ne


Ba matsalace ta na'ura ko wani abu ba, mummunan hari ne daga hackers, kuma wannan shine hari mafi muni da kamfanin ya taba fuskanta tun bayan kafuwarsa, sau biyu kenan kamfanin na fuskantar hari cikin wannan shekara ta 2021


Daga lokacin da Facebook da WhatsApp Instagram suka dena aikin na tsawon awa 6 kamfanin ya tafka asaran kudi ya rasa kimanin Dalar Amurka Bilyan 7, wanda yayi daidai da Naira Tiriliyon 3, kamar yadda jaridar Bloomberg ta ruwaito


Ba shakka tsarin da facebook suke da shi na nuna wariya ga wadanda basa so suna dakatar da account dinsu, da shiga sabgar siyasar diplomasiyya na wasu shugabannin duniya zai kaisu ya baro watan watarana.

Wannan hari da suka fuskanta zai sa suyi karatun ta nutsu


Wannan abinda ya faru da facebook izna ce ga mutanen da suka mayar da facebook hanyar neman kudi ta kowace irin hanya mai kyau da marar kyau, duk wani abinda aka samar dashi a duniya bai da tabbatas, watarana zai gushe


Hankalin mutane ya tashi sosai bayan da facebook, WhatsApp da Instagram suka dena aiki, mutane sun shiga damuwa, nasha kiran waya har sai da na gaji na kashe wayata, saboda mutane suna ganin abin yazo bagtatan ba tare da sun shirya ba, to kamar hakane mutuwa zata riskemu a kowani lokaci, don haka muyi tanadin mutuwa jama'a


Allah Ya kyautata Karshen mu

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment