Min menu

Pages

FG zata bada 50k ga ɗaliban NCE, da 75k ga Ɗaliban dake karanta “Education” a jami’o’in Gwamnati

 FG zata bada 50k ga ɗaliban NCE, da 75k ga Ɗaliban dake karanta “Education” a jami’o’in Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta amince da bada Naira dubu 75,000 a matsayin tallafin karatu a duk zangon karatu, ga ɗaliban dake karanta digiri akan nazarin ilmi wato-Education a jami’o’in gwamnatin tarayya na Nigeria.Haka zalika, masu karatun NCE zasu samu tallafin karatu na Naira dubu 50,000 a matsayin wani ƙoƙari na janyo masu hazaka da basira ya zuwa ga koyarwa, kamar yadda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya alƙawurta.Ministan Ilmi Adamu Adamu wanda Babban Sakataren shi ya karanta jawabanshi Sonny Echono, yace ma’aikatar zata haɗa hannu da gwamnatocin jahohi domin ɗaukar ɗaliban da suka kammala karatu aiki kai tsaye.


Yace “Ɗaliban dake karanta digiri na B.Ed/B.A Ed/Bsc a jami’o’in Gwamnatin tarayya zasu samu tallafin karatu na Naira dubu 75,000 duk zangon karatu na semester, a yayinda ɗalibai masu karanta NCE zasu samu Naira dubu 50,000.


“Gwamnatin Tarayya zata gano wasu hanyoyi, wanda gwamnatocin jahohi zasu bayar da aiki kai tsaye ga masu karanta NCE a matakin Firamare.

Comments