Min menu

Pages

Hanyar da harkers suke bi suke yin harking din Facebook account din mutane.

 Hanyar da harkers suke bi suke yin harking din Facebook account din mutane.Akwai hanyoyi da dama da harkers suke bi suke kwace account din mutane amma yanzu saboda lokaci zamu fadi guda daya ne mai sauki wanda kuma mutane basu gane harkers ne ke yawan irin wannan ba.


Sauda dama ana yawan ganin photo haka kamar bidiyo na mace dana miji tsirara sai ace idan mutum yana son kallon wannan bidiyon cikakke dole ya shiga wannan Link din da suka ajiye.


Wasu da dama a cikin mutane suna son kallon irin wannan bidiyon dan haka mutane da dama suna danna wannan Link din domin kallon bidiyon wanda daga karshe zai kaisu can cikin blog dinsu, wanda su kuma zasu sake cewa duk wanda yake son kallo dole saiya cike duk wasu bayanansa.


Wasu suna sanya bayaninsu wanda hakan ba karamin kuskure bane, wanda da wannan bayanan harkers ke bi wajen kwace account din mutane.


Dan haka daga zarar mutum ya shiga irin wannan Link din yayi saurin canja password dinsa.Comments