Min menu

Pages

e-Naira Currency: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Kaddamar Da Kudin Internet na CBN

e-Naira Currency
e-Naira Currency

E-Naira Currency Kudin Internet Na Bankin CBN

A yaune 25 ga watan October 2021, Shugaba Muhammadu ya kaddamar da sabon tsarin kudin Internet wanda babban bankin Najeriya CBN yafito dashi, kamar yadda ya bayyana wannan kudin zai kawo saukin mu'amala da kuma kasuwancin zamani bugu da kari kudin e-Naira zai habaka tattalin arzikin Nigeria.

Amma Menene e-Naira Currency?

E-Naira kamar Cryptocurrency ne wato Bitcoin sai dai yasha bambam dashi saboda wannan kudi yana karkashin bankin CBN ne wanda kuma shine yake kula da gudanarwasa, sabanin Bitcoin, Ethereum da sauransu basu da mai gudanarwa.

Sannan sauran kudin Internet na zamani da ake amfani dasu suna tashi da sauka wanda shi kuma e-Naira baya hawa ko sauka kamar dai yadda Naira take, don haka wannan kudi amfani dashi babu kasada kamar sauran Coin din zamani.

Yadda Zaka Saya Da Kuma Ajiye E-Naira Currency

Bankin CBN ya tanadi wata jaka (e-Naira Speed Wallet) wanda idan kasayi kudin zaka tarashi aciki kuma wannan jaka tana da tsaro sosai don haka baka da fargabar kwacewa, wannan jaka yanzu haka zaka iya samunta a manhajar Playstore ga masu amfani da Android ko kuma Appstore ga masu amfani da Iphone.

Sannan wannan jaka kamar asusun ajiya ne na banki (Bank Account) sai dai shi wannan yana karkashin kulawar CBN ne kadai, da E-Naira Speed Wallet zaka iya ajiye kudi da kuma turawa wasu wanda suke bukatar E-Naira Currency.

Yadda Zaka Mallaki E-Naira Currency

Idan kana bukatar mallakar wannan kudi zakayi download na eNaira Wallet Speed sannan zakaga inda zakayi rijista da cikakkun bayananka wanda suke bukata kafin bankin CBN ya amince dakai, bayanan da ake nema sune: Bank Name & Account Number, BVN, Date of Birth, da kuma sauran abubuwa wanda sai kaje zaka gansu.

Wani abu mai muhimmanci daya kamata kasani, bazaka iya cire kudin enaira kamar yadda ake cirewa a ATM ba, sai dai zaka iya tura kudin daga manhajar bankinka zuwa e-Naira Wallet ko kuma daga manhajar bankin zuwa wannan jaka ta enaira.

e-Naira Currency
e-Naira Currency Muhammadu Buhari


Abubuwa Guda 3 Naci Gaba Da E-Naira Currency Zai Kawo

1. Zai Kawo Saurin hada hadar cinikayya da kuma saukin sayan duk wani kaya anan Nigeria dama sauran kasashen ketare, sannan zai bawa masu aiki a Internet (Online Business) damar maki dayawa.

2. Zai Saukaka nauyin da gwamnatin Nigeria take dauka wajen buga kudin takarda da kuma rarraba wadannan kudade, saboda shi wannan kudi gaba daya ana aiki dashi a Online don haka baka bukatar yawo dashi kamar sauran kudin Najeriya.

3. E-Naira Currency yana da tsaro sosai wanda bankin CBN yabashi domin gujewa 'yan damfara, babu wanda ya isa ya buga jabun eNaira kamar yadda akeyiwa Naira kuma wannan kudi zai karawa Nigeria hanyar samun haraji kwarai da gaske.

Wannan Shine e-Naira Currency Atakaice?

Wannan shine bayanin kudin Internet wanda bankin CBN ya kirkira wato E-Naira Currency, kuci gaba da bibiyayar wannan website domin samun karin bayani akan wannan kudi. 

Sannan zamu kawo hanyoyin daza kayi amfani dashi domin samun kudin shiga. Kukasance da www.duniyarlabari.com

Comments