Min menu

Pages

Za a tafka ruwan saman da ba'a taba yin irinsa ba yau a arewacin Nigeria tare da iska mai karfi.

Za a tafka ruwan saman da ba'a taba yin irinsa ba yau a arewacin Nigeria tare da iska mai karfi.Hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya ta ce yau Talata za'a tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ba'a taba yinsa ba a tarihin Najeriya ruwan zai taso dauke da iska mai karfin gaske tun daga yankin tafkin Chadi, ya mamaye sassan Arewa kasar.


Bari muji daga bakin yan Najeriya, shin ko an fara yin wannan gagarumin ruwa a yankunanku yanzu, mu dai a nan sashin an fara don kuwa yanzu haka gari ya dau harami kuma ana ta sheka ruwa.


Idan an fara a garin da kuke muna son ku fadamana sunan ku da adireshin ku sannan ku aiko mana da hotunan yadda aka wayi gari a inda kuke domin sakawa a shafinmu.


Muna fatan Allah ya saukar mana da ruwan ni'ima ya kuma kare gidaje da garuruwa ameen.

Comments