Min menu

Pages

Mai Kudin Duniya Jeff Bezos Ya Gano Maganin Dake Hana Tsufa

 Mai Kudin Duniya Jeff Bezos Ya Gano Maganin Dake Hana Tsufa Fitaccen attajiri dan kasar Amurka Jeff Bezos wanda aka ce yafi kowa kudi a duniya, ya gano wani magani wanda zai sanya mutum ya rayu har illa masha Allah ba tare da ya tsufa ba.


Shi dai wannan magani an kirkiro shi ne a wani katafaren dakin gwajagwajen kimiyyar halittu da aka kashe masa sama da dalar Amurka miliyan 270 domin inganta shi da kayan aiki, anyi amfani da kwararren mai gwajegwaje inda ya kirkiro wani sinadari da aka yi amfani da shi a jikin bera, kuma aka gano beran baya girma tunda aka yi amfani da sinadarin a jikinsa, yayin da aka samu wani beran da ba a sanya masa sinadarin ba kuma aka ga yana girma.


Binciken dai ya nuna za a iya amfani da sinadarin a jikin Bil adama kuma yayi aiki, ba tare da mutum ya tsufa ko kamanninsa sun canja ba.


Jaridar Daily Mail ta kasar Burtaniya ce ta ruwaito labarin.

Comments