Min menu

Pages

Wani dan kwallon kasar France ya mutu bayan ya shafe shekaru 39 a sume saboda wannan dalilin

 Wani dan kwallon kasar France ya mutu bayan ya shafe shekaru 39 a sume saboda wannan dalilinDan wasan PSG da kasar France Adams ya mutu Bayan daya shafe shekaru 39 a sume tare da tallafin inji:


An tabbatar da cewa tsohon Dan wasan PSG da kasar France Jean-Pierre Adams ya mutu  Bayan ya shafe shekaru 39 a sume. Adams ya fada Suma ne a watan March na shekarar 1982  Bayan da likitansa yayi wani kuskure a lokacin Yana Masa aiki a gwiwarsa.Dan wasan ya samu rauni ne a gwiwarsa inda akasa ranar 17 ga watan March na shekarar 1982 a matsayin ranar da za'a Masa aiki a asibitin Édouard Herriot Hospital dake birnin Lyon. Ana tsaka da aikin ne likitan nasa yayi wani kuskure inda hakan ya janyowa Dan wasan shafe shekaru 39 a sume, tare da tallafin inji.

Comments