Min menu

Pages

Yadda zaku iya amfani da wayoyin hannunku a matsayin remote na Tv din gidajenku

 Yadda zaku iya amfani da wayoyin hannunku a matsayin remote na Tv din gidajenku



A wasu gidajen akan yawan rasa remote na Tv saboda yara sun dauka sun jefa shi wani waje ko kuma wani abu yasa an rasa shi kasancewar sa wani abu mai yawan sammatsi hakan yasa ake yawan rasa shi.

Wanda idan aka rasa shi kuma shikenan sai anyi ta nema ko ansha fama kafin ayi kallo ko kamo wani abu da wannan tv din, dan haka mukai bincike muka kawo muku wata hanya wacce za kuyi amfani da wayoyin hannunku ku mayar dasu kamar remote din tv dinku wajen canja tasha ko kamowa.



Dan haka ga hanyar da zaku bi domin yin amfani da wayoyin hannunku a matsayin remote control dinku

Farko kuje Play store sannan sai ku rubuta universal Tv remote control zasu nuno muku kala daban daban, saiku zabi na farkon wanda suka nuna muku.


Bayan kun dauko application dinnan sai kuyi installed dinsa.


Bayan kunyi installed din saiku bude shi sannan sannan zaku ga wani guri an rubuta IR TV Remote saiku danna shi, zai nuna muku inda zaku zabi model din TV din taku shikenan.



Sannan ga Link din da zaku dauko wannan application din zamu ajiye muku a kasa 


                    Download Apps


                        Download



Comments