Min menu

Pages

Adam A. Zango Ya Saba Auren Yaransa Mata Ni Ba Irinsu Ba Ce, Inji Ummi Rahab

 Adam A. Zango Ya Saba Auren Yaransa Mata Ni Ba Irinsu Ba Ce, Inji Ummi RahabBayan ƙura ta lafa a dambarwar dake tsakanin jarumi Adam A. Zango da ƴar ɗakin sa Ummi Rahab, a karon farko jarumar ta yi magana tun bayan fara dambarwar, inda a jiya ta samu tattaunawa da jaridar Daily Trust kan abin da ke tsakanin ta da Adam A. Zango.


A cikin hirar Ummi Rahab ta bayyana cewa har yanzu tana ɗaukar Adam A. Zango a matsayin Uba, kuma tana girmama shi, amma kowa ya kama hanyar sa ba batun sake tafiya tare.


Haka zalika tayi ƙarin haske kan cire ta da yayi daga cikin shirin “Farin Wata Sha Kallo”, inda ta bayyana yana da damar saka duk wanda ya so a fim din sa da cire duk wanda ya so ba ta da matsala da hakan, amma ta danganta hakan da kishin kula samarin da take, ya kuma yi ƙoƙarin hana ta taƙi hanuwa yasa shi yayi abinda yayi.


Ummi Rahab ta bayyana cewa ita baza ta iya auren shi ba tunda yana matsayin uba a wajenta, inda tace shi kuma ya gaza fahimtar hakan, ta ce ya saba da auren yaran sa mata da yake fim da su, sai dai ita ba haka take ba tana da ikon yin yadda ta so da rayuwar ta, indai tsarin bai saɓawa shari’a ba.


Ummi Rahab ta kuma musanta batun cewa da yayi yana bata tarbiyyya, inda har ta bada misali da sanda yasa ta saka wasu kaya da suka jawo mata zargi a fim ɗin sa. A cewar ta bai cancanci a kira shi da mutum mai nagartar da zai bada tarbiyya ba.Comments