Min menu

Pages

Gargadi ga duk masu amfani da manhajar Google chrome

 Gargadi ga duk masu amfani da manhajar Google chromeGa wata sanarwa ko kuma gargadi ga duk masu amfani da manhajar Google chrome, kamfanin google na mika sanarwa ga duk masu amfani da manhajar Google chrome din dasu zama cikin shiri domin an samu masu satar bayanai wato harkers sunyi kutse cikin manhajar ta google chrome din.


Dan haka kamfanin yake gargadar masu amfani da manhajar domin ya sanar musu da samuwar masu kutsen da suka sako kai cikin manhajar Google chrome din.

Kamar yadda kusan kowa ya sani manhajar Google chrome kusan itace babbar hanyar yin bincike da sauran abubuwa na amfanin mutane a bangaren online.

Wannan yasa koda yaushe kamfanin yake fuskantar matsin lamba ga masu son yi masa kutse a cikin manhajar tasa domin samun damar da za'a shiga domin diban bayanan mutane wanda hakan bazai yiwa mutane dadi ba.


Domin ko yanzu an samu karuwar zero guda biyu a yadda suke harhada bayanai wanda Mai manhajar yace baisan dasu ba, hakan shine ya bashi damar sanin cewa ana kokarin yin kutse ne cikin tsarin dan haka yai saurin ankarar da masu amfani da manhajar tasa koda zasu ga sabun wasu abubuwa.


Dan haka ku kasance cikin shiri duk da cewa muna yin bakin kokarin mu ganin mun shawo kan wannan matsalar  wanda bazata shafi duk wani mai amfani da manhajar ba inji mai kamfanin..Comments