Min menu

Pages

Masu GbWhatsApp ya kamata kuyi hankali da wannan

 Masu Gbwhatsapp ya kamata kuyi hankali da wannan



Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana wasu tsaruka da 'Whatsapp' na asali ba shi da su, kamar irinsu adana (saving) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga 'status(es)' na mutane kai tsaye, ko ɓoye alamar karantawa ko karbar sako, ko don yana nuna alamar in mutum na online, ko don tura 'file' mai nauyi, ko ɓoye groups/chats, ko rubuta sunan 'group' da harafai sama da 35, yin status da harrafai 250; a taƙaice, GB yana da wasu ‘features’ da whatsapp.com ba shi da su.

Amma, ka san duk waɗannan tarko ne na masu datse? Sun tsara shi ne ta yadda zai baka sha’awa sosai, fiye da manhajar ta asali (normal Whatsapp), tare da baka damar wasan ɓoyo da ma’abota amfani da Whatsapp, musamma ma ƴan uwa mata, ka tura saƙo, a karanta, amma ba zaka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status ɗinka ba tare da ga wanda ya gani ba...

Tom! Maganar gaskiya kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne; ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an ƙirƙire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba.

Ina gargaɗar masu amfani da GB, ko son amfani da shi, da su ƙauracewa manhajar saboda (wasu daga cikin) dalilai kamar haka:

• Na farko, GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AlexMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ƙa’idar ƙirƙirar da bada lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba zaka sami manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taɓa ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.

• Na biyu, mai amfani da GBWhatsapp, ya yi sani, duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya leƙawa ba, siyarwa, ko amfani da ba shi a duk lokacin da suka dama.

• Na uku, idan aka turo ma wani sako mai ɗauke da ‘virus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa 'spyware' ne.

• Na huɗu, duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi yasa, yawanci waɗanda ake musu kutse (hacking) ta Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YO… da sauransu.

• Na biyar, GBWhatsapp baya restore (dawo da bayanai) a wasu lokutan, kamar yadda na faɗa a sama, asali manhajar ta saɓawa tsarin Google, kuma ana backup ne (yawanci) da Google account. Shi ya sa, da zarar ya yi 'expire' (wani lokaci) zaka rasa duk bayananka, har 'groups' da kake ciki, sai ka nemi a maida ka.

• Na shida, ka lura, a duk lokacin da ka ɗauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargaɗeka cewa, wannan app din zai iya cutar da kai, ko bayananka; baka taɓa lura ba? In ka taɓa lura da haka, don me zaka sa kanka a halaka?

Kar ku yaudaru! GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma a kowanne lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin.

Comments