Min menu

Pages

Yadda zaku sanya wayoyinku suna yin caji da wuri

 Yadda zaku sanya wayoyinku suna yin caji da wuriAssalamu alaikum da fatan kuna lafiya, hakika muna jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu muna godiya.

A yau cikin shirin namu muna tafe ne da wasu hanyoyi wanda zaku bi ku sanya wayoyinku suna yin caji da wuri.


Saboda mutane da yawa suna damuwa ganin cewa idan suka sanya wayarsu a caji tana jimawa sosai ba tare da ta cika ba, wani kuma sai kuga wayarsa saita kwana a jikin wuta amma kuma bata cika ba.


Dan haka muka zo muku da wasu yan hanyoyi wanda idan har kuka bi to da wuri wayarku zata cika idan kuka sanyata a gurin caji.


√ Ka sanya cajin wayar a jikin socket ba a jikin computer ba:- Wani lokacin sai kuga mutane suna sanya cajin wayarsu a jikin computer bayan da cewa ga socket nan wannan yana hana waya ta cika da wuri.


√ ka kashe wayarka:- Duk lokacin da zaka sanya caji ya kasance ka kashe wayar domin masana bincike a bangaren waya sunce waya idan tana a kashe tafi saurin yin caji.


√ Kada kana amfani da wayar lokacin da take caji, domin hakan yana hana waya cika da wuri kuma yana taba lafiyar waya.


√ Ka samu charger mai kyau yar dauka, domin tana da matukar mahimmanci kuma tana sanya waya ta cika da wuri sannan tana karawa batir na wayar kwari.


Wadannan sune hanyoyin da bincike ya nuna kuma su mutum zai bi idan har yana son wayarsa tana saurin yin caji da wuri.

Comments