Min menu

Pages

Kuyi saurin rufe wadannan guraren a cikin setting na wayoyinku

 Kuyi saurin rufe wadannan guraren a cikin setting na wayoyinkuAkwai gurare masu yawa daya kamata ku rufe su idan a bude suke a cikin wayoyinku saboda abubuwan da barinsu a buden yake kawo wa.


Wani lokacin muna zaune da waya bamu sani ba akwai abubuwan da a cikin wayar ake samunsu wasu su karawa wayar lafiya wasu kuma su dakusar da aikin da take baza su bata damar gabatar da aiki cikin sauri ko kuma a gaggauce ba.


Wani sa'in muna ganin wayoyinmu suna yin nauyi ko kuma muga space dinsu ya cika ba tare da munsan abinda ya cika mana kan wayar ba.


Dan haka muka zo muku da wasu gurare a cikin wayoyinku wanda ya kamata ku kashe su idan a kunne suke domin zai taimaka wajen gyara lafiyar battery na wayoyinku sannan zasu sanya wayoyinku yin aiki ba tare da sunyi nauyi ba, sannan kuma za susa storage din wayarku baza su cika da wuri ba.

Wadannan sune jerin guraren da zaku kashe a cikin setting din wayoyinku


√ Ku kashe nan gurin ( Nearby Device Scanning ) idan a kunne yake


 √ Ku kashe nan gurin (Usage And Diagnostic Information ) idan a kunne yake

 √ Wannan gurin (Ad Personalization ) din shima idan a kunne yake ku kashe shi.

√ Shima nan gurin da zaku ga an rubuta ( Improve Accuracy ) ku kashe shi idan a kunne yake

√ Ku kashe gurin (Google Location History )

√ Akwai gurin da zakuga an rubuta ( Network Data Analytics) shima saiku kashe gurin


√ Za kuga wani guri an rubuta ( Install Unknown Apps) saiku kashe gurin idan a kunne yake.

Duka wadannan guraren a cikin setting suke dalilin da yasa bamu kawo muku bidiyon ba shine kowacce waya tanada bambanci da wata amma dai idan kun duba cikin setting zaku gansu.

Mun gode.

Comments

1 comment
Post a Comment
  1. Thanks so much team for the jobs you people are doing, My advice is next time please if possible you include the exact places we will find each of this, you mention in settings, will helps us to go directly and do the needful thanks usman bla tarab.

    ReplyDelete

Post a Comment