Min menu

Pages

Zanfi maida hankali akan abincin dabbobi fiye dana mutane inji sabon ministan noma

 Zanfi maida hankali akan abincin dabbobi fiye dana mutane inji sabon ministan noma



Sabon Ministan Harkokin Noma Mohammed Abubakar ya bayyana cewa gwamnati za ta bayar da tallafi sosai ga masu manya da ƙananan masu sarrafa abincin dabbobi, domin su kakkafa masana’antun su ya yankunan karkara.


Ya ce hakan na da nasabar cewa a yankunan karkara ne ake samun kayan gonar da ake amfani da su ana samar da abincin dabbobin.


Minista Abubakar ya bayyana haka a ranar Alhamis, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Noma, Ernest Umakhihe, a wurin Babban Taron Samar da Abincin Dabbobi na Ƙasa.


Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ƙara ilmantar da manoma hanyoyin dabarun kiwon dabbobi na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi a zamanance.


“Gwamnatin Tarayya za ta hanzarta fara aiwatar da shirin ta na samar da kuɗaɗe da kayan aiki ga manya da ƙananan masu samar da abincin dabbobi, domin su shiga cikin yankunan karkara su kafa masana’antun samar da abinci a faɗin ƙasar nan.


“Kuma za ta tallafa wa cibiyoyin bincike domin su fito da sabbin dabarun samar da abincin dabbobi, yadda hakan zai magance matsalar tsadar abincin dabbobin a faɗin ƙasar nan.” Inji Minista.


Sabon ministan ya ce yayin da ya ke shiga ofishin kwanan nan, zai maida hankali wajen bunƙasa dabarun kiwon dabbobi da samar da abinci da kuma sauran matsalolin da su ka dabaibaye harkokin noma, waɗanda ya ce sun haɗa har da matsalar tsaro.


Ya ce daga shekarar 1957 zuwa yanzu, Najeriya na da sama da masana’antar sarrafa abincin dabbobi fiye da 1000.


Ya ce yawan na su ne ya kai Najeriya ita ce ƙasa ta 40 a duniya, cikin jerin ƙasashen da ke da yawan masana’antun sarrafa abincin dabbobi.


Ya ce tilas Najeriya ta tashi tsaye sosai wajen bunƙasawa da kuma dabarun samar da abincin dabbobi, wanda shi ne ƙashin bayan samar da tattalin arziki wajen kiwon dabbobi, kaji da kifaye

Comments