Min menu

Pages

Tsananin Kyau Na Ya Sanya Maza Ke Guduna, Har Hanzu Bani Da Saurayi Cewar Hauwa

 Tsananin Kyau Na Ya Sanya Maza Ke Guduna, Har Hanzu Bani Da Saurayi Cewar HauwaBudurwa ta shiga damuwa matuka, akan yadda samari ke gudunta maimakon su dinga rububin zuwa wajenta.


Budurwar mai suna Hauwa tace ta rasa dalilin da ya sanya mazan suke ta faman gudunta saboda tsananin kyawun da Allah yayi mata.


A wani rubutu da ta wallafa da yake ta faman yawo a shafukan sada zumunta, kyakkyawar budurwar ta bayyana rashin jin dadinta akan kyawun da take dashi, inda tace shine babban dalilin da ya sanya har yanzu bata da saurayi.


Ta ce a lokuta da dama samari sukan turo mata sako na cewa suna sonta, kuma zasu kari rayuwarsu da ita, amma da abu yayi nisa sai su gudu, baza ta kara ji daga garesu ba.


Tsoron su shine kada sai suna cikin soyayya dani wani yazo ya kwace ni. Hakan ya sanya suke jin tsoro, kuma suke guduwa.


“Sun ce kyauna yana basu tsoro, saboda wani namijin kan iya zuwa ya dauke ni, kuma hakan ya sanya basa jin za su iya cigaba da soyayya dani,” Hauwa ta wallafa.


Lokacin da ta fara girma, Hauwa ta samu mutane da yawan gaske da suka nuna soyayyarsu a kanta, amma da ta girma yanzu duk sun gudu.


“Dana fara girma, mutane suna matukar sona, kuma suna kula dani sosai, har ya sanya ni jin dadi cewa ina da matukar masoya, amma dana cika ‘ya mace, sai na gano cewa kyau na bashi da wani amfani,” cewar Hauwa.


Ta ce tana ji tana gani sa’anninta suke yin aure, amma ita babu dama.


“Ina ji ina gani kawayena suke yin aure, amma ni hakan ya gagara. Maza ko da yaushe suna nesanta kansu dani, suna cewa kyauna yayi yawa, inda suke cewa sun tabbata suna ji suna gani wani zai zo ya kwace ni, saboda sun tabbata idon mutane da yawa yana kaina, saboda haka da wuri za a iya kwace ni.

Sunana Hauwa, daga jihar Adamawa, ni kuma Bafulatana ce,” ta rubuta.

Comments