Min menu

Pages

Yankin Arewacin Najeriya Zai Shiga Cikin Halin Mafi Zama da Yunwa a Duniya~Inji WFP

 Yankin Arewacin Najeriya Zai Shiga Cikin Halin Mafi Zama da Yunwa a Duniya~Inji WFPKungiyar abunci ta duniya WFP ta sanya yankin Arewacin Najeriya na daya daga cikin wuraren da al'umma zasu fuskanci matsin yunwa a kwanakin nan.


WFP ta ce, tana matukar tausayawa al'ummomin dake cikin yankin Arewa domin zasu shiga cikin halin zama da yunwa mafi tashin hankali.


Majalisar dunkin duniya ta nemi hukumomin bayar da agajin gaugawa na kasashe da su hanzarta kaiwa Arewacin Najeriya tallafin abunci tun kamin su tsunbula cikin halin yunwa.


Hukumar ta kula da abunci na duniya WFP ta bayyana cewar, halin rashin zama lafiya da yankin Arewa ke fuskanta yana daya daga cikin dalilan da zasu sa al'ummar yankin su shiga cikin yunwa a yan kwanakin nan.


Comments