Min menu

Pages

Yadda Na Haɗu Da Hushpuppi Har Na Yi Masa Dillancin Riguna Da Huluna – Abba Kyari

 Yadda Na Haɗu Da Hushpuppi Har Na Yi Masa Dillancin Riguna Da Huluna – Abba Kyari



“Abbas wanda daga baya mu ka gano ana kiran sa Hushpuppi, ya kira ofishin mu kamar shekaru biyu da su ka gabata. Ya yi ƙorafin cewa wani a nan Najeriya ya yi barazanar zai kashe shi da iyalan sa a nan Najeriya. 


Kuma ya aiko mana lambar wayar mutumin, ya roƙi mu gaggauta ɗaukar mataki tun kafin ya kai ga kashe iyalan na sa.


“Mun je mun gano inda wanda ake zargin ya ke, mu ka yi bincike kuma mu ka gano gaskiyar magana babu wata barazanar kisa a lamarin. Ashe ma abokan juna ne tsawon shekaru masu yawa. 


Kawai dai saɓani ne ya shiga tsakanin su a kan kuɗi. Daga nan mu ka saki wanda ake zargin a kan beli. Ko kulle shi ma ba a ba.


“Babu wanda ya nemi ko sisi a hannun Hushpuppi. Mu a lokacin babban aikin mu shi ne mu hana wanda aka ce zai yi kisa aikata abin da aka ce mana zai aikata ɗin.


“To daga nan sai ya ga wasu hotuna da na ke sanye da kayan gargajiya a shafi na na soshiyal midiya. Ya ce ya na buƙata. Na haɗa shi da tela na, ya aika wa telan N300,000 a asusun telan na banki. 


Aka ɗinka masa kaya da kuma huluna biyar. Daga nan ya aiko wani ya karɓar masa a ofishin mu.


“Don haka masu ƙoƙarin ɓata mana suna har su na cewa mun karɓi maƙudan kuɗaɗe a hannun Hushpuppi, za su ji kunya. 


Domin ba mu tsoma hannun mu cikin dagwalon kuɗaɗen harƙalla ba, kamar yadda wasu ke watsawa.” Inji Kyari.


Majiya Premium Times Hausa:

Comments