Min menu

Pages

Zamu kori duk wani Ma'aikaci da muka kama yana fidda takardun Gwamnati a Kafafen Sadarwa na zamani--inji Gwamnatin Tarayya

 Zamu kori duk wani Ma'aikaci da muka kama yana fidda takardun Gwamnati a Kafafen Sadarwa na zamani--inji Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta koka akan yawaitar fitar da takardun ta ba bisa ka'ida ba, a Kafafen Sadarwa na zamani da sauran wasu wurare.


A saboda Haka, tayi gargadin korar Ma'aikatan da aka kama da haka.


 Shugabar Ma'aikatan Tarayya Dr Folasade Yemi-Esan tayi gargadin, a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 2 ga watan ogustan Shekarar 2021.


Sanarwar tace, wannan sau biyu kenan, da Shugabar Ma'aikatan tayi gargadi a cikin shekara daya, a cikin wata sanarwa guda biyu a watan Maris na Shekarar 2020.


A wata sanarwa, Yemi-Esan tace ofishin ta zai dogara da wasu dokoki na aikin Gwamnati, wajen korar Wanda suka cigaba da wasa da aikin su, tare da fitar da takardun Gwamnati.


Sanarwar ta kara dacewa "Hankalin ofishin Shugabar Ma'aikatan Tarayya akan yadda ake yawaitar fitar da Takardu masu Mahimmanci na Gwamnati a Kafafen Sadarwa na zamani.

Comments