Min menu

Pages

Wata Sabuwar Cuta mai saurin kisa ta 'bulla Afirka

Wata Sabuwar Cuta mai saurin  kisa ta 'bulla Afirka 

Hukumomi a Kasar Guinea sun tabbatar da samun mutum na farko daya kamu da wata cuta mai Suna Marburg, wadda ta kasance cuta ce Mai saurin kisa, a yankin Afirka ta Yamma, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana a ranar Litinin.


"Yanayin bazuwar cutar Marburg, dole ne muyi gaggawar tsaida ita, tun tana matakin farko," inji Dr Matshidiso Moeti, Daraktan shiyya na Hukumar WHO a Afirka.


Ana iya yada cutar tsakanin mutum ta hanyar haduwar jini, da kuma ta hanyar 'kofofin jiki musamman ta hanyar zufar jiki.


Cutar Marburg, cuta ce wadda Kwayoyin Virus ke janyo wa, inda take haifar da Zazzabi, kaikayi, da Ciwon Kai, gami da kaikayin fata a matakin Farko.


Haka Zalika, idan ciwo ya tsananta, zai haifar da Zazzabi Mai zafi da kuma mutuwa baki daya.


Ana iya kamuwa da cutar idan mutum ya cudanya da Biri da sauran su, kari bisa ga hada jiki da Wanda ke fama da cutar.


Yawan wadanda suka mutu yakai kimanin kashi 23-90, inda cutar Marburg na iya haifar da cutar ido, kunne, gami da fitar jini.


Ana cigaba da bincike akan cutar, a yayinda Kasashen Afirka ke cigaba da bincike akan cututtuka wadanda ake saurin dauka, dalilin yawaitar cudanya da Dabbobi na yankin.

Comments