Min menu

Pages

Wannan shine abinda yasa zango ya kori Ummi rahab daga gidansa kuma ya cire ta daga cikin film dinsa na farin wata sha kallo

 Wannan shine abinda yasa zango ya kori Ummi rahab daga gidansa kuma ya cire ta daga cikin film dinsa na farin wata sha kalloCikin satin nan abubuwa sun cika kafafen yada labarai cewar Adam a zango ya kori Ummi rahab daga gidansa harma ya cireta daga cikin film dinsa na farin wata sha kallo, saidai har yanzu mutane basu da masaniyar dalilin da yasa hakan ya faru.

Wasu nata maganganu suna dora laifin akan Adam a zango yayinda wasu kuma ke dora laifin a kan ita yarinyar.Ummi rahab dai za muce kusan a matsayin ya take a gun Adam a zango, ko kuma muce a matsayin ya ya dauketa domin itama abba take ce masa, tun bayan sunyi wani shirin film mai suna Ummi inda a lokacin yarinyar tana karama kuma ta fito ne a matsayin yar gidan Adam a zango.

To daga karshe bayan yarinyar ta girma ta dawo masana'antar kannywood din saita koma gidansa inda har ya sanyata cikin wani shiri da yake me suna FARIN WATA SHA KALLO.

Yarinyar ta sanu matuka kasancewar ta mai kyau da kuma nuna tan da shi jarumin yayi.


Ta samu tarin masoya daga cikin samari wasu ma yan kannywood dinne, ganin cewar mutane masu yawa suna zuwa ko kuma cewa suna sonta yasa Adam a zango ya fara sanya ido domin ganin suwa ye ke mu'amula da ita.

To daga karshe ya sameta domin ya mata magana domin daga cikin wasu da take mu'amula dasu bai aminta da su ba, ganin cewa yana mata yawan magana yasa take ganin cewa kamar yana shiga mata hanci ne daga kudundune. Wannan yasa suka dan fara samun tangarda har mai afkuwa ta afku suka watse.


Wanda daga karshe shi ya goge duk wasu photunan yarinyar a shafinsa itama ta goge nasa sannan kuma ya kawo wata jaruma da ta maye gurbinta a shirin da yake dauka.


Majiyar ta rawaito cewar yanzu haka yarinyar tana soyayya ne da wani mawaki dan kaduna mai suna lilinbaba.


To koma dai menene Allah ne masani

Comments