Min menu

Pages

WATA SABUWA:-INA IYAYEN UMMI RAHAB ?

 INA IYAYEN UMMI RAHAB ?DAGA Datti Assalafiy 


Satin da ya gabata na ga wani labari dake cewa shahararren 'dan wasan Hausa film Adam Zango ya kori wata matashiyar 'yar Hausa film mai suna Ummi Rahab saboda wasu dalilai da ba'a bayyana ba


Sannan sai jiya kuma naga wani labarin wai Ummi Rahab ta cewa Adam Zango "Na ji kana fada cewa wai kana so ka bani tarbiyya amma na bijire maka, idan ka cigaba da neman bata mini suna da wannan sharrin  wallahi zan tona maka asiri"


Jaridu sun ruwaito wannan labarin a matsayin raddi da gargadin da Ummi Rahab ta yiwa tsohon Maigidanta Adam Zango, ba wanda ya san me ya hadosu, idan labarin ya tabbata gaskiya, nafi ganin tausayin Ummi Rahab akan Adam Zango, yarinyace mai kyawun sura wanda idan batayi hankali ba tsoffin kuraye mayu zasu ragargaje mata rayuwa su watsar kamar yadda suka yiwa Maryam Boot


Yara 'yan mata kanana irin wannan, a lokacin da suke tashen balaga, suna falli sakamakon hulda da suke da manyan mutane kudi yana shiga musu ta kowani lungu da sako, ji suke tamkar kasa ba zata iya daukar su ba saboda girman kai, basa jin nasiha da shawara, sun fi yadda duniya ta koya musu darasi ba mutane ba


Ina iyayen Ummi Rahab? mu yasa kuka bar 'yar ku ta shiga Hausa film?

Danyar yarinya kamar wannan ba daidai bane iyayenta ku kyale ta tana yawon gararamba ba tare da idonku yana kanta ba


Idan labarin nan ya tabbata gaskiya Ummi Rahab ta yiwa Adam Zango gargadi da barazanan zata tona masa asiri to akwai abin dubawa anan


Wani irin boyayyen asiri ne ga Adam Zango wanda ta sani idan ta bayyana zata wargaza masa lissafi?


Zina yayi da ita ta dauki bidiyon sa kamar yadda artificial karuwai na yanzu suke yi?

Ko kuma ciki ya mata ya zubar shiyasa tayi barazanan tona masa asiri kamar yadda aka ruwaito?


ba laifi bane ayi irin wannan tambayar


Ku bata shawara taje tayi aure ya fi mata rufin asiri da kima da mutunci, sana'ar film ba inda zai kaita sai tashar da na sani marar amfani

Comments