Min menu

Pages


Shin wacece Ummi rahab? Da tarihinta Kyakkyawar jaruma Ummi Rahab na daya daga cikin matasan jarumai da tauraruwar su ke haskawa a wannan lokaci a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.

Wacece Ummi Rahab

An haifi jaruma Ummi Rahab a ranar 7 ga watan Afrilun shekarar 2003, a jihar Kaduna dake Arewacin Najeriya. Ta yi karatu a matakin Firamare da Sakandare a jihar ta Kaduna.

Yadda Ummi Rahab ta shiga harkar fim

Sakamakon shakuwa da kuma kauna dake tsakanin Ummi Rahab da fitaccen jarumi Adam A Zango, ya sanya har ya zuwa yanzu wasu ba su yadda cewa Ummi ba diyar Adam A Zango ba ce, tun bayan fitowar ta a cikin fim din “Ummi”, lokacin tana karamar yarinya.Fim din Ummi na daya daga cikin fina-finan da jarumar ta fara fitowa, tun daga lokacin kuma ta yi sanyi ba a sake jin duriyar ta ba sai a ‘yan shekarun nan.


Bayan Ummi Rahab ta girma, Adam A Zango ya sake dawowa da ita harkar fim, inda ya sanya ta a cikin shirin fim din “Farin Wata Sha Kallo” wanda ya sanya ta sake daukaka a cikin masana’antar.


Iyayen Ummi Rahab

Kamar yadda muka bayyana a baya cewa mutane na ganin cewa Jarumi Adam A Zango shine mahaifin a gare ta, jarumin ya fito ya musanta wannan magana, sai dai kuma har ya zuwa yanzu babu wani rahoto dake nu ni da ainahin iyayenta.

A rahoton da Neptune Prime suka ruwaito, wakilin su Saleh Inuwa ya ruwaito cewa jarumi Adam A Zango ba shi da wata dangantaka da ita, inda ya ce jarumin ya dauko ta daga wajen wata fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da bai bayyana sunanta ba.

Masu kallon fina-finan Hausa dai sun cigaba da sanya matsin lamba ga hukumar MOPPAN domin ta kirawo Zango da Ummi domin su yiwa duniya bayanin ainahin abinda ke tsakanin su.

Ummi Rahab da Adam A Zango sun raba gari

Wasu bayanai da ke ta faman yawo na nuni da cewa alaka tayi tsami tsakanin su inda hakan zai bawa mutane da dama mamaki, ganin cewa tun kafin a je ko ina an samu wannan baraka tsakanin Zango da Rahab wacce ya dauka tamkar diya a wajen shi. Har ya zuwa yanzu wasu ba su yadda cewa Ummi ba diyar Adam A Zango ba ce, tun bayan fitowar ta a cikin fim din “Ummi”, lokacin tana karamar yarinya.

Bayan Ummi Rahab ta girma, Adam A Zango ya sake dawowa da ita harkar fim, inda ya sanya ta a cikin shirin fim din “Farin Wata Sha Kallo” wanda ya sanya ta sake daukaka a cikin masana’antar. To amma sai dai kafin a shiga daukar kashi na biyu na shirin, gayyatar ta watse tsakanin su.


Comments