Min menu

Pages

An fasa daura auren wata budurwa da angonta saboda likita yace tana da HIV

 An fasa daura auren wata budurwa da angonta saboda likita yace tana da HIV




Rahotanni daga jihar Taraba na cewa an fasa daura auren wata budurwa mai suna Yusra da angon ta mai suna Auwal biyo bayan sakamakon binciken lafiya da likita ya gabatar a zauren daura auren wanda ya nuna cewa amaryar tana dauke da cutar HIV.


Kamar yadda kuka sani bisa al’ada kafin a daura aure ana kawo sakamakon binciken lafiya daga bangaren augo da amarya domin gudun raduwar cututtuka a cikin al’umma, sai dai irin wannan bincike wani lokacin ya kan bar baya da kura saboda ana samun rahotannin fasa yin aure daga sassa daban daban sakamakon irin wannan bincike, ko a watannin da suka gabata ma.


Saida jaridar Manuniya ta bada rahoton fasa wani aure sakamakon binciken da ya nuna shima amaryar tana dauke da cutar ga rahoton jaridar na baya.


An shiga matsananciyar tashin hankali yau a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna sakamakon fasa daura wani auren wani matashi Sabiu (mun canza sunansa na asali) da akayi bayan waliyyin amarya da wakilin ango sun hallara har an kammala shigar da siga da komi da komi.


Wakilin Manuniya wanda ya halarci daura auren da aka yi a wani wuri a garin ya ce bayan an kammala shigar da siga za a daura auren sai mai daurawar ya bukaci a gabatar masa da takardar shaidar gwajin lafiya na Amarya Ramusa’u (mun cenza suna ba sunan ta na asali bane) da Angon ta Sabiu


Manuniya ta ruwaito bayan da aka ce babu sai limamin ya ce ba zai daura auren ba sai da takardar lafiya saboda haka ya bukaci za a jira har sai ango da amaryar sunje sunyi gwaji sun kawo masa takardar sahidar asibiti inda nan da nan ango da amarya suka bazama asibiti akayi masu gwaji a mabambantan asibiti.


To sai dai bayan wani lokaci sai ango da wakilinsa suka bayyana a wajen daura auren dauke da takardarsu ta shaidar gwaji amma abun mamaki sai aka ji waliyyin amarya shiru.


Manuniya ta ruwaito nan akayi ta kai ruwa rana har zuwa jimawa amma waliyyin amarya ya ce mahaifiyar amarya taki bashi takardar shaidar lafiyar diyarta har dai daga bisani aka gano ashe sakamakon gwaji ya nuna amarya na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.


Wakilin Manuniya ya ce “Nan da nan aka fasa daura auren inda hayaniya ta kacame amma daga bisani waliyyin amarya suka kira ango da wakilinsa inda suke shaida masa gaskiyar magana sakamakon gwaji ya nuna amarya fa tana dauke da HIV”

Comments