Min menu

Pages

Wannan abinda Shehu Dahiru Bauchi yayi ya bawa mutane mamaki l

 ALHERIN ALLAH YA KAIWA SHEHU DAHIRU USMAN BAUCHIKamar yadda na ga labarin, ance ba da jimawa ba Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi diran mikiya daga jirgin sama a birnin tarayya Abuja domin ganawa da Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya akan kisan gillar da arna suka yiwa 'yan uwa Musulmai a Jos


Tsakani da Allah wannan matakin da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya dauka ya burgeni matuka, hakan zaisa Gwamnati ta dauki abin da muhimmanci


Haka ya kamata shugabannin Musulmi su zama, shugabannin addinin Musulunci a Nigeria suna da tasirin da zasu iya dakatar da komai a Kasarnan har sai anbi kadin jinin 'yan uwa Musulmai da aka zubar a Jos, tsoro ba na Musulmai bane


Allah Ka karawa Shehu Dahiru Bauchi lafiya da imani, Allah Ka sa wannan ya zama sanadin kawo karshen kisan gillar da arna suke yiwa Musulmai a Jos Amin

Comments