Min menu

Pages

TA FADA RIJIYA SABODA ZA AI MATA KISHIYA

TA FADA RIJIYA SABODA ZA AI MATA KISHIYA
Wata mata da ke zaune a garin Azare jihar Bauchi ta dira rijiya saboda tsananin bacin rai.


Matar wacce 'yar uwarta ta nemi Zuma Times Hausa ta sakaye sunanta yayin tattaunawarmu ta ce, "tushen matsalar ta fara ne lokacin da mijinta ya ce zai kara aure, amma ta ce ba ta yarda ba sai dai in ya zaba ko karin aure ko ya sake ta, shi kuma ya ce ba zai dauki ko daya daga cikin zabin da ta ba shi ba.

don haka ta tattara kayanta a jaka ta nufi gidansu da yaranta biyu.


Sai dai cikin rashin sa'a zuwanta gidan bai amfane ta da komai ba sai sabon bacin rai don kuwa da aka tambaye ta me ya hada su da mijin har ta dawo gida ta ce musu akan zai kara aure ne sai iyayen suka hau ta da zagi har yayanta yana cewa idan ba ta koma dakinta ba sai yayi mata dukan tsiya.


'Yar uwar ta ci gaba da fadawa Zuma Times Hausa cewa, "ko da ta dawo dakinta ma ba ta fasa cewa mijin ya sauwake mata ba amma mijin ya ja tunga akan bai ga mai zai sa shi ya saketa ba."


Bayan ya fita ne ita ma ta fice daga gidan babu maya fi ta dira cikin wata tsohuwar rijiya ashe danta ya biyo bayanta.


Ganin haka nan yaro ya tsandara ihu da kururuwar mamansa ta fada rijiya.


An dai yi nasarar fito da ita da ranta kai tsaye aka kai ta asibiti ta samu manyan raunuka da targade uku a yatsunta na kafa da hannu inda

A yanzu haka dai ana zargin wakila dai aljanu ne suka sa ta afka rijiyar.


Wannan laifin aljannu ne bakin kishi?

Comments