Min menu

Pages

INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNW WataBudurwa Ta Mutu Suna Tsaka Da Fasikanci A Cikin Mota

 INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UNW WataBudurwa Ta Mutu Suna Tsaka Da Fasikanci A Cikin MotaDailytrust ta ruwaito cewa Mutuwa ta riski wata budurwa a yayin da suke tsaka da fasikanci da saurayinta a cikin mota.


An garzaya da budurwar mai shekara 15 zuwa asibiti ne bayan saurayin nata da yake fasikanci da ita ya lura cewa ta fita daga hayyacinta.


'Yan sanda da ke binciken lamarin sun ce saurayin, wanda ake kira “babban mai taimako”, ya shaida musu cewa yana cikin saduwa da ita a cikin mota ne ya lura labbanta da fatar jikinta sun koma fari fat, hannuwanta kuma sun jujjuye.


Ko da aka kai ta asibiti, likitoci sun gano zuciyarta ta buga, amma babu yadda suka iya, washegari da safe kuma ta ce ga garinku nan.


Labarin mutuwar buduwar a yayin da suke fasikanci da saurayinta ya girgiza ’yan uwa da abokan arziki da ma makwabta a unuguwar Cubatão da ke birnin São Paulo na kasar Brazil.


A halin yanzu, likitoci a asibitin suna gudanar da bincike a kan gawar domin gano tabbatar da ainihin musabbabin mutuwarta, ’yan sanda kuma na nan suna jiran sakamako.


Iyayenta sun shaida wa ’yan sanda cewa ’yarsu ba ta fama da matsalar bugun zuciya kuma ba su san saurayin nata ba. 


Likitocin a sibitin na UPA Jardim Casquiero da ke yankin na Cubatão sun ce a gwajin farko da suka yi an samu jini a cikin al’aurar budurwar, amma babu alamar an ci zarafinta.Comments