Min menu

Pages

Karanta Sabbin Jahohi 20 da za'a kirkira a Nigeria

 Karanta Sabbin Jahohi 20 da za'a kirkira a Nigeria

Kwamitin Majalisar Dattawa akan sake dubi akan Kundin tsarin Mulki ya bada shawarar a kirkiri sabbin Jahohi 20 a cikin Nigeria.


Haka Zalika, sun kuma bukaci kirkiro da baiwa Jahohin damar zabar Wanda suke so, daga Hukumar Zabe mai Zaman Kanta.


Jahohin da suka bukaci a kirkira sun hada da; Jahar ITAI, wadda za'a fitar daga Jahar Akwa Ibom, sai Jahar Katagum, za'a fitar da'ita daga Jahar Bauchi, sai Jahar Okura, za'a fitar da'ita daga Jahar Kogi ta Gabas, da kuma Jahar Adada, za'a cire ta daga cikin Jahar Enugu,  da kuma Jahar Gurara za'a fitar da'ita daga Jahar Kaduna ta Kudu, gami da Jahar Ijebu za'a fitar da'ita daga Jahar Ogun.


Akwai kuma Jahar Ibadan za'a fitar da'ita daga Jahar Oyo, sai Jahar Tiga, daga cikin Jahar Kano, da Jahar Ghari za'a fitar da'ita daga Jahar Kano, sai kuma Jahar Amana za'a fitar da'ita daga Jahar Adamawa, sai kuma Jahar Gongola za'a kirkire ta daga Jahar Adamawa.


Sai Jahar Mambilla za'a kirkire ta daga Jahar Taraba, sai Jahar Savannah za'a fitar da'ita daga Jahar Borno, sai Jahar Okun za'a kirkire ta daga cikin Jahar Kogi, da kuma Jahar Etiti za'a fitar  da'ita daga cikin yankin Kudu maso Gabas.


Sauran Jahohin sun kunshi, kirkirar Jahar Orashi daga cikin Jahohin Imo da Anambara, sai Jahar Njaba daga cikin Jahar Imo, ko kuma a fitar da Jahar Aba daga cikin Jahar Abia, da Jahar Anioma za'a fitar da'ita daga cikin Jahar Delta, sai kuma Jahar Torogbene da kuma Jahar Oil River za'a fitar dasu daga cikin Jahohin Bayelsa, da Delta da Jahar River, gami da kirkirar Jahar Bayajida daga cikin Jahohin Katsina da Jigawa da Zamfara.


Tunda Farko, Majalisar Dokoki ta Kasa ta yiwa kudirin yin gyaran fuska ga Kundin tsarin Mulki na Shekarar 1999 karatu na biyu, domin kirkirar Yansandan Jahohi da Jami'an tsaro na shiyya.


Shugaban Kwamitin Majalisar akan Bangaren Shari'a, Wanda ya gabatar da kudirin, ya bayyana cewa kudirin na bukatar "kirkirar Yansandan Jahohi da kuma sauran Jami'an tsaro domin inganta Harkokin tsaron rayuka da Dukiyoyin Al'ummar Nigeria.

Comments